Majalisa Ta Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Gaggauta Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga a Jihar Arewa

Majalisa Ta Buƙaci Shugaba Tinubu Ya Gaggauta Kawo Ƙarshen Ƴan Bindiga a Jihar Arewa

  • Majalisar wakilai ta ƙasa ta buƙaci Bola Tinubu ya gaggauta umurtan jami'an tsaro su kawo ƙarshen ta'addancin ƴan bindiga a jihar Katsina
  • Wannan ya biyo bayan kudirin gaggawa da ɗan majalisar tarayya daga Katsina, Sada Soli, ya gabatar kan halin da mutane ke ciki a jihar
  • Ya shaida wa majalisar yadda wasu gungun ƴan bindiga ke kokarin kwace iko da wasu yankuna, yana mai cewa ya kamata a tashi tsaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauki matakin kawo karshen ayyukan ƴan bindiga a jihar Katsina.

Majalisar ta bukaci Tinubu ya umarci jami'an tsaro su ƙara zage dantse kan masu aikata laifukan ta'addanci a Katsina da sauran sassan Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugabannin majalisa za su gana da Shugaba Tinubu, bayanai sun fito

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
"Ka Magance Yan Bindiga a Jihar Katsina" Majalisar Wakilai Ga Tinubu Hoto: HouseNGR
Asali: Twitter

Wannan kiran dai ya biyo bayan kudirin gaggawa mai muhimmancin ga kasa wanda Honorabul Sada Soli, ɗan majalisa daga Katsina ya gabatar a zaman majalisar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake gabatar da kudirin, Soli ya bayyana damuwarsa game da illar da ayyukan ‘yan bindiga ke yi a rayuwar al’ummar jihar Katsina, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Ya kara da cewa taɓarɓarewar tsaro a Katsina ya jawo asarar rayuka da lalata dukiyoyi da kuma yin garkuwa da mutane maza da mata da kananan yara a kowace rana.

Ɗan majalisar tarayyan ya ce har yanzu hukumomin tsaro ba su dauki mataki na gaggawa da nufin magance matsalolin tsaron da suka dabaibaye jihar Katsina.

Ya yi kira da a kara tura jami’an tsaro zuwa yankunan da abin ya shafa domin yakar ‘yan fashin dajin da kuma dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Minista: Dakarun sojoji sun hallaka manyan ƴan bindiga 7 da suka addabi mutane a Najeriya

Ya kuma bayyana cewa wasu gungun ‘yan bindiga da suka fito daga Kaduna da Zamfara da ke makwabtaka da jihar suna kokarin ƙwace iko da wasu kauyuka a Katsina.

Wane mataki majalisar ta ɗauka kan kudirin?

Majalisar ta yi shirun minti ɗaya domin girmama waɗanda aka kashe a Katsina kana ta umarci hukumar agaji NEMA da ma'aikatar jin ƙai su kai tallafi ga yankunan da abun ya shafa.

Ta kuma yabawa rundunar sojoji bisa samamen da suka kai kananan hukumomin Safana da Kurfi, inda suka kashe manyan ƴan bindiga biyu ranar Litinin.

Mataimakin gwamnan Edo na tsaka mai wuya

A wani rahoton na daban Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu na shirin rasa kujerarsa bayan majalisar dokokin jihar ta fara shirin tsige shi.

Majalisar dai ta aike da takardar fara shirin tsige Shaibu inda zai mayar da martani kan zarge-zargen da ake masa cikin kwanaki bakwai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel