'Ƴan Bindiga Sun Kashe Tsohon Shugaban Hukumar Gwamnati da Wasu Mutum 2

'Ƴan Bindiga Sun Kashe Tsohon Shugaban Hukumar Gwamnati da Wasu Mutum 2

  • Wasu mahara da ake zaton ƴan fashi ne sun kashe mutum 3 ciki har da tsohon manajan darakta na hukumar gidaje ta jihar Jigawa
  • Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin a yankin ƙaramar hukumar Birnin Kudu ranar Talata da daddare
  • Mai magana da yawun ƴan sandan Jigawa, DSP Lawal Shiisu, ya ce dakarun ƴan sanda sun baza komarsu domin kama maharan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Jigawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce wasu ƴan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe mutane uku a karamar hukumar Birnin Kudu.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), DSP Lawan Shiisu, ya fitar ranar Laraba a Dutse.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe mutane sama da 15, sun tafka mummunar ɓarna ana dab da azumi a jihar Arewa

Yan bindiga sun kashe mutum uku a Jigawa.
Yan Fashi Sun Harbe Mutun Uku Har Lahira a Jihar Jigawa, Sun Sace Babur Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

A rahoton Daily Trust, kakakin ƴan sandan ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ranar Talata mun samu labari daga kauyen Iggi cewa an ga wasu ƴan bindiga uku a kan babur ɗaya a yankin Iyayi na jihar Bauchi sun tunkaro kauyen Iggi da ke Birnin Kudu.
"Nan take aka tura ƴan sanda zuwa yankin kuma aka sanar da jami'an tsaro musamman ƴan banga. Da karfe 10:15 na dare muka sake samun rahoto daga Warwade duk a Birnin Kudu cewa waɗannan ƴan bindigar sun kwace babur."

Maharan sun kashe mutum 3

Shiisu ya ƙara da cewa maharan sun kuma buɗe wuta kan wata mota da ta tunkaro su mai ɗauke da fasinjoji huɗu.

Nan take suka kashe direban motar, Hassan Garba da fasinjoji biyu, Garba Maiwake da Shehu Saidu, rahoton Daily Post.

Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce tuni aka ajiye gawarwakin a dakin ajiyar gawa na cibiyar kiwon lafiya ta tarayya (FMC) da ke Birnin Kudu.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da ƴan bindiga suka kashe ƴan sanda da yawa a babban birnin jihar APC

A cewarsa, dakarun ƴan sanda sun bazama sintiri kurfa-kurfa da nufin cafko waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa direban motar, Hassan Garba, bai jima da ajiye aiki ba a Jigawa. Shi ne tsohon shugaban hukumar gidaje.

Yadda lamarin ya faru

Wani mazaunin Birnin Kudu, Malam Aminu Aminu, ya shaidawa Legit Hausa cewa abinda ya faru ya yi matuƙar tada musu hankali.

Da yake bayanin yadda lamarin ya faru yayin hira da wakilin mu, Aminu ya ce:

"Eh (Hassan Garba) baban wani abokina ne da muka yi makaranta tare, to ya je gona ya sallami waɗanda suka masa aiki, sai ya ga wasu mutane a jejin kuma dama ana masa ɓarna.
"Shi ne ya haske su da fitilar mota, to ashe ƴan iska ne, wasu na ganin Fulani ne, suka buɗe wa motar wuta, su huɗu ne a motar amma mutum ɗaya ne ya sha.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta, sun kashe mutum 7 ƴan gida 1 da wasu bayin Allah

"Wanda ya tsira dabara ya yi, ya kwanta a ciki kamar ya mutu, da suka tafi shi ne ya shi ya dawo gida. Abun ba daɗi kwanta-kwata, Allah ya mana maganin su."

Yan fashi sun shiga bankuna biyu a Kogi

A wani rahoton na daban Ƴan bindiga sun farmaki ofishin ƴan sanda da bankuna biyu a jihar Kogi, sun kashe ɗan sanda ɗaya da wani bawan Allah mai talla a bakin titi

Ganau sun bayyana cewa maharan sun biyo wata motar ɗauko kudi daga wani banki, kuma sun kwashe adadi mai yawa da ba a tantance ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel