Sojojin Najeriya Sun Aike da Muhimmin Saƙo Ga Musulmai Yayin da Ake Shirin Fara Azumin Ramadan

Sojojin Najeriya Sun Aike da Muhimmin Saƙo Ga Musulmai Yayin da Ake Shirin Fara Azumin Ramadan

  • Hedikwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta bayyana cewa sojoji sun shirya tunkarar kowace irin barazana musamman a watan Ramadan
  • A wata sanawar da DHQ ta fitar ranar Jumu'a, ta ce sojoji ba zasu yi kasa a guiwa ba sai sun ga bayan ƴan ta'adda baki ɗaya a kasar nan
  • Hediwata ta ce sojoji mutane ne masu son zaman lafiya, za su yi duk mai yiwuwa wajen samar da kwanciyar hankali a ko ina ake buƙata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedikwatar tsaro (DHQ) ta ce dakarun sojojin da aka tura a fadin Najeriya sun shirya tsaf domin tunkarar duk wata barazanan tsaro a kasar nan.

DHQ ta kuma tabbatar da cewa sojojin a shirye suke su tunkari duk wata barazana musamman a lokacin da al'ummar musulmi ke shirin fara azumin watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Minista: Dakarun sojoji sun hallaka manyan ƴan bindiga 7 da suka addabi mutane a Najeriya

Babban hafsan tsaron Najeriya, Christopher Musa.
Sojoji a shirye suke don tunkarar barazanar tsaro a lokacin Ramadan - DHQ Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta tattaro cewa hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun DHQ na ƙasa, Manjo Janar Buba Edward, ya fitar ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dakarun sojoji sun shirya kuma za su iya magance duk wata barazanar tsaro a tsawon lokacin da za a shafe ana azumtar watan Ramadan.

"Yayin da ake shirye-shiryen fara azumin watan Ramadan, dakarun sojoji sun shirya tunkarar kowace irin barazana kuma sun san yadda za su kawar da ita.

Mun shirya kawo karshen ta'addanci - DHQ

Buba ya kuma sha alwashin cewa sojojin ba za su yi kasa a gwiwa ba ko su huta har sai sun kakkaɓe ‘yan ta’adda gaba ɗaya a fagen daga.

A rahoton Leadership, ya ce:

“Sojoji za su ci gaba da kakkaɓe ‘yan ta’adda da masu taimaka masu da ke fagen daga tare da korarsu daga wuraren da suka ɓuya a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

An rasa rai yayin da dakarun sojoji suka gwabza da ƴan bindiga, sun samu babbar nasara a Arewa

"Rundunar sojoji tana kaunar zaman lafiya kuma tana kokarin tabbatar da kwanciyar hankali a duk inda buƙatar hakan ta taso a faɗin kasar nan.
"Saboda mun shirya tsaf kuma muna nan kan bakarmu na kare kasar nan da mutanen cikinta."

Uba Sani ya yi magana kan manyan matsaloli 2

A wani rahoton kuma Malam Uba Sani ya bayyana cewa hanyoyin da ake bi da nufin magance talauci da matsalar tsaro a Najeriya kuskure ne.

Gwamnan ya ce waɗannan kalubalen biyu sun zama alaƙaƙai da ke damun shugabannin siyasa a halin yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel