Ana Ba Tsaro a Kasa, Akpabio Ya Fito Ya Fadi Ci Gaban da Tinubu Ya Kawo a Bangaren

Ana Ba Tsaro a Kasa, Akpabio Ya Fito Ya Fadi Ci Gaban da Tinubu Ya Kawo a Bangaren

  • Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa tsaro ya inganta sosai a mulkin Tinubu
  • Sanata Akpabio ya yi nuni da cewa tun bayan da Tinubu ya hau kan mulki an samu raguwar manyan kashe-kashe a ƙasar nan
  • Ya bayyana cewa hare-haren da ake samu a yanzu koma baya ne amma nan ba jimawa ba za su zama tarihi gaba ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa matsalar rashin tsaro ta ragu matuƙa a ƙasar nan tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

Akpabio ya bayyana haka ne a lokacin da yake bayar da gudummuwa a yayin muhawara kan ƙudirin da ya shafi kashe-kashen da aka yi a jihar Benuwai, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

"Babu ruwan Tinubu" Minista ya fallasa ainihin waɗanda suka jefa ƴan Najeriya a wahala da yunwa

Akpabio ya yi magana kan rashin tsaro
Akpabio ya ce an samu tsaro sosai a mulkin Tinubu Hoto: Godswill Obot Akpabio, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya yi nuni da cewa yayin da sabon harin ya kasance koma baya ne, an sami raguwar yawaitar manyan kashe-kashe a faɗin ƙasar nan, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Emmanuel Udende ne ya ɗauki nauyin wannan ƙudiri.

Me Akpabio ya ce kan rashin tsaro?

A kalamansa:

"Aiki na farko da ke kan gwamnatin jiha shi ne ta yi amfani da kuɗaɗen tsaro wajen ganin an kare tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar Benuwai."
"Tsarin farko shi ne gwamnatin Benuwai, kamar yadda Sanata Udende ya nuna, ba mu ji wani abu daga gare ta ba."
"Idan an kashe mutum 50 aka kuma kai wa al’umma hari, za mu yi tsammanin gwamnatin jihar za ta shirya tsare-tsare tare da jami’an tsaron da ke a jihar da abin ya shafa, su ga abin da za su iya yi kafin a kawo wa shugaban ƙasa Bola Tinubu."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ministan Tinubu ya fadi dalili 1 da ya sa mutanen yankinsa ba za su yi zanga-zanga ba

"Ina so na tabbatar maku cewa Shugaba Tinubu, duk da cewa bai daɗe da zama a ofis ba, yana goyon bayan ayyukan rundunar soji."
"A gaskiya tun da ya hau kan karagar mulki, rashin tsaro ya ragu, kuma ba a sake kai manyan hare-hare ba, amma wannan lamarin koma baya ne kawai, kuma za a kawo ƙarshensa."

Shugabannin majalisa za su gana da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin majalisar tarayya za su gana da shugaban ƙasa mai girma Bola Ahmed Tinubu.

Shugabannin majalisar za su gane da shugaban ƙasar ne kan matsalar rashin tsaron da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel