Tashin Hankali Yayin da Ƴan Bindiga Suka Kashe Yan Sanda da Yawa a Babban Birnin Jihar APC

Tashin Hankali Yayin da Ƴan Bindiga Suka Kashe Yan Sanda da Yawa a Babban Birnin Jihar APC

  • Ƴan bindiga sun yi ajalin jami'an ƴan sanda aƙalla 5 da wasu ƴan mata biyu a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi ranar Jumu'a
  • Rahotanni sun bayyana cewa a shekarar da ta gabata, ƴan bindiga sun kashe jami'an tsaro a daidai wurin da suka sake kashe wasu yau
  • Har yanzun rundunar ƴan sanda ba ta fitar da sanarwa a hukumance kan wannan lamari ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ebonyi - Wasu hatsabiban ƴan bindiga sun halaka aƙalla jami'an ƴan sanda biyar a Abakaliki, babban birnin jihar Ebonyi ranar Jumu'a, 8 ga watan Maris, 2024.

Jaridar Daily Trust ta ce lamarin ya faru ne a babbar gadar Ebya da ke kan titin Hilltop a birnin Abakaliki da misalin karfe 5 na safiyar ranar Juma’a.

Kara karanta wannan

'Ƴan bindiga sun kashe tsohon shugaban hukumar gwamnati da wasu mutum 2

Yan bindiga sun kashe ƴan sanda a Ebonyi.
Yan Bindiga Sun Kashe Jami'an Yan Sanda a Babban Birnin Jihar Ebonyi Hoto: PoliceNG
Asali: Facebook

Haka kuma maharan sun kashe wasu mata biyu da ake zargin karuwai ne yayin da suke kokarin komawa cikin gidajensu a yankin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton Vanguard ya tattaro cewa a kwanakin baya ƴan bindiga sun kai farmaki wannan wuri kuma sun kashe jami'an ƴan sanda kusan watanni uku da suka wuce.

Dakarun ƴan sandan da suka rasa rayuwarsu suna bakin aiki ne lokacin da ƴan bindigan suka buɗe musu wuta ba zato ba tsammani.

Yadda maharan suka kashe jami'an tsaro

Wata mata a yankin mai suna Misis Ngozi ta shaida wa wakilin jaridar cewa maharan sun dawo daga kai hari ne a lokacin da suka bude wuta kan jami’an.

Ngozi ta ce:

"Yankinmu ya zama wurin da tsageru ke yawan kai hare-hare, a safiyar yau na ji wani labarin cewa wasu ‘yan bindiga sun kashe ‘yan sanda a titin Hill-Top kusa da gidan mai.

Kara karanta wannan

Majalisa ta yi magana kan matan da aka sace a Borno, ta tabo jami'an tsaro

"Kuma kun san cewa irin wannan lamari ya faru a daidai wannan wuri a bara, inda wasu gungun ‘yan bindiga suka halaka jami’an ‘yan sanda.
Har yanzu ba a yi jana'izar wasu yan sandan da aka kashe a harin bara ba, kuma a yanzu gashi an ƙara kashe wasu shida, ciki har da 'yan mata biyu a safiyar yau."

Matar ta ƙara da cewa ana raɗe-raɗin ƴan matan da aka kashe suna tare da ƴan sandan ne yayin da wasu ke cewa karuwai ne zasu koma gida.

Kawo yanzu jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Joshua Ukandu, bai fitar da wata sanarwa ba game da wannan mummunan lamari.

An kashe mutum 3 a jihar Jigawa

A wani rahoton kuma wasu mahara da ake zaton ƴan fashi ne sun kashe mutum 3 ciki har da tsohon manajan darakta na hukumar gidaje ta jihar Jigawa.

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin a yankin ƙaramar hukumar Birnin Kudu ranar Talata da daddare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel