Daga Neman Itace: 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sace 'Yan Gudun Hijira 319 a Arewa

Daga Neman Itace: 'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Sace 'Yan Gudun Hijira 319 a Arewa

  • An shiga jimami a jihar Borno bayan ƴan ta'addan Boko Haram sun sake tafka mummunar ta'asa a jihar
  • Tsagerun masu ɗauke da makamai sun yi awon gaba da mata ƴan gudun hijira har guda 319 a garin Ngala na jihar
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an sace matan ne bayan sun shiga cikin daji nemo itacen da za su yi amfani da su

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Ƴan ta'addan Boko Haram sun sace mata ƴan gudun hijira har 319 a jihar Borno.

Jaridar Daily Trust ta ce wata majiya mai tushe ta tabbatar mata da cewa an sace ƴan gudun hijiran ne a garin Ngala, hedikwatar ƙaramar hukumar Gambarou Ngala ta jihar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hotuna sun bayyana yayin da aka gudanar da salloli na musamman a Zaria

'Yan ta'adda sun sace 'yan gudun hijira
Tsagerun Boko Haram sun sace mata 'yan gudun hijira a Borno Hoto: @govborno
Asali: Twitter

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da sace mutanen amma ta ce adadin mutanen da aka sace ba su kai 319 ba, inda majiyar tace adadin da suka ji an sace bai wuce mutum 113.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Boko Haram: Yadda lamarin ya auku

Sai dai wata majiya daga sansanin ƴan gudun hijira na Babban Sansani, ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadin da ta gabata, bayan matan sun je ɗiban itace a daji domin yin amfani da shi da sayarwa.

A kalamansa:

"Ƴan ta’addan sun kewaye su ne a dajin Bula kunte da ke yammacin garin Ngala. Sun ƙyale tsofaffi sannan suka tafi cikin daji tare da ƴan mata 319 da wasu samari.
"Amma, uku daga cikin ƴan matan da suka tsere suka koma Ngala sun ce ƴan ta'addan sun kai su wani daji kusa da ƙauyen Bukar-mairam a Jamhuriyar Chadi.

Kara karanta wannan

Rigima ta ƙara zafi a APC yayin da dakarun ƴan sanda suka ƙwace iko da sakateriya a jihar Arewa

"Sun tsere ne da daddare bayan da ƴan ta’addan suka yi barci, sun yi tafiya ta tsawon kwanaki biyu kafin su isa Ngala."
"Yawancin ƴan matan da aka sace daga sansanin Babban Sansani ne, sauran kuma daga sansanin Zulum da Arabic.
"Sun je daji nemo itace domin sayarwa saboda abincin da muke samu daga sansanin bai isa ya ciyar da mu ba. Rayuwa tana da wahala a nan."

An yi gargaɗi kan shiga daji saboda Boko Haram

Wata majiya daga jami’an tsaron ta ce a ko da yaushe suna gargadin ƴan gudun hijirar kan zuwa wasu yankuna a cikin daji saboda fargabar kai hari.

A cewar majiyar:

"Muna gargadinsu koyaushe da su kasance cikin wuraren da suke da tsaro, amma matsin tattalin arziƙi ne ya tilasta yawancinsu suka tafi. Ba su da wata hanyar samun kuɗaɗe da ta wuce sare bishiyoyi don sayarwa."

Wannan dai na ɗaya daga cikin manya-manyan sace-sacen da aka yi a Borno, tun bayan sace ƴan mata 276 na makaranta sakandaren ƴan mata ta gwamnati da ke Chibok, a daren 14 ga watan Afrilun 2014.

Kara karanta wannan

Babbar nasara: Asirin wasu ƴan bindiga 15 ya tonu, sun fara sakin bayanai a jihar Arewa

Mayaƙan ISWAP Sun Halaka Manoma

A wani labarin kuma, kun ji cewa mayaƙan ƙungiyar ƴan ta'adda ta ISWAP sun kai farmaki kan manoma a jihar Borno.

Miyagun ƴan ta'addan sun halaka mutum uku a yayin harin da suka kai a ƙaramar hukumar Damboa ta jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel