Dakarun Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga Sama da 200, Sun Samu Manyan Nasarori a Najeriya

Dakarun Sojoji Sun Kashe Ƴan Bindiga Sama da 200, Sun Samu Manyan Nasarori a Najeriya

  • Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun yi nasarar halaka ƴan ta'adda 210 tare da kamo wasu 142 da ceto mutum 46 da aka yi garkuwa da su
  • Hedkwatar tsaro ta ƙasa DHQ ce ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar kan nasarorin da sojoji suka samu a mako ɗaya da ya gabata
  • Edward Buba, mai magana da yawun DHQ ya ce sojojin sun shirya tsaf domin tunkarar duk wata barazana da kawo karshen ta'addanci a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa dakarun sojoji da ke aikin cikin gida a fadin kasar nan sun kashe 'yan ta'adda 210 a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun aike da muhimmin saƙo ga musulmai yayin da ake shirin fara azumin Ramadan

Bayan haka kuma sojojin sun kama ƴan ta'adda 142 kana suka ceto mutane 46 da aka yi garkuwa da su cikin mako ɗaya, kamar yadda Leadership ta tattaro.

Babban hafsan tsaro, CDS Christopher Musa.
Sojoji Sun Halaka Yan Bindiga Sama da 200, Sun kamo 142 Tare da Ceto Mutum 46 Hoto: HQ Nigeria Army
Asali: Facebook

Daraktan yaɗa labarai da hulda da jama'a na DHQ, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Jumu'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sojojin sun kuma kama wasu mutane 66 da ake zargin barayin mai ne tare da kwato lita 1,932,245 na danyen mai da aka sace.

Dakarun sojin ba su tsaya iya nan ba, sun kwato lita 432,150 na tataccen AGO da aka tace ba bisa ka'ida ba, da kuma lita 3,500 na DPK da suka kai darajar an2.2bn.

Dakarun sojin sun kwato muggan makamai

Buba ya ƙara da cewa sojojin sun kwato makamai iri-iri guda 243 da alburusai kala daban-daban guda 5,453 a tsawon wannan lokaci na mako ɗaya, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Jirgin rundunar sojin saman Najeriya ya gamu da hatsari a Kaduna, bayanai sun fito

Kakakin DHQ ya ce sojoji ba zasu yi ƙasa a guiwa ba, za su ci gaba da kawar ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga tare da kakkabe su daga maboyarsu a fadin kasar nan.

Manjo Janar Buba ya ƙara da cewa dakarun sojojin sun shirya tsaf a matsayin runduna domin tunkarar duk wata barazana kuma sun san yadda zasu kawar da ita.

An kashe rayuka a jihar Jigawa

A wani rahoton kuma wasu mahara da ake zaton ƴan fashi ne sun kashe mutum 3 ciki har da tsohon manajan darakta na hukumar gidaje ta jihar Jigawa.

Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin a yankin ƙaramar hukumar Birnin Kudu ranar Talata da daddare

Asali: Legit.ng

Online view pixel