Gwamnatin tarayyar Najeriya
Gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ta fara biyan albashin malaman jami'o'i na kungiyar ASUU da aka rike saboda yajin aikin da suka yi.
Gwamnatin Tarayya ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai yi murabus ba saboda tsadar rayuwa da wahala da 'yan Najeriya ke fama da shi a halin yanzu.
wamnonin jam'iyyar PDP sun nemi gwamnatin jam'iyyar APC da ta yi murabus daga mulki idan har ba za ta iya magance tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar ba.
Hukumar kula da kare hakkin masu amfani da kayayyaki ta kasa (FCCPC) ta sake bude kantin siyayya na Sahad da ta rufe a yankin Garki, babban birnin Abuja.
Bashir Ahmad, tsohon hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce kantin Sahad da aka rufe na daya daga cikin kantuna mafi saukin kaya a babban birnin Abuja.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roki gwamnoni jihohi su kashe kuɗaɗen da suke samu ta hanyar biyan ma'aikata hakkinsu amma kada su kashe al'umma.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinibu, ya sa labule ga gwamnonin jihohin Najeriya kan batun tsadar rayuwa da kuma harkokin tsaro da ke ƙara taɓarɓarewa a sassan ƙasa.
Naira ta fadi zuwa N1,600 idan aka kwatanta da dala a ranar Alhamis yayin da tattalin arzikin Najeriya ke ci gaba da tabarbarewa a karkashin Shugaba Bola Tinubu.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da gwamnoni sun fara yunƙurin kafa rundunar ƴan sandan jihohi da nufin magance duk wata matsala ta tsaro a ƙasar nan.
Gwamnatin tarayyar Najeriya
Samu kari