Dirama Yayin da Wasu Sanatoci Suka Tafka Kuskure a Zaman Gabatar da Kasafin Kuɗin 2024

Dirama Yayin da Wasu Sanatoci Suka Tafka Kuskure a Zaman Gabatar da Kasafin Kuɗin 2024

  • Wata dirama ta auku a zauren majalisar tarayya gabanin isowar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ranar Laraba
  • Wasu sanatoci da basu fahimci yadda ake zaman haɗin guiwa ba, sun wuce zauren majalisar wakilai bisa kuskure
  • Sai dai bayan gane babban kuskuren da suka tafka, nan take sanatocin suka yi hanzarin fita zuwa majalisar dattawa

FCT Abuja - Wata ƴar karamar dirama da auku bisa rashin sani yayin da ake shirye-shiryen haɗa mambobin majalisar wakilai da sanatoci wuri ɗaya kan kasafin kuɗin 2024.

Zauren majalisar wakilan tarayya.
Dirama Yayin da Wasu Sanatoci Suka Shiga Zaman Majalisar Wakilai Bisa Rashin Sani Hoto: HouseNGR
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne yayin da wasu Sanatoci suka shiga zaman majalisar wakilai, wanda haka ya saɓa wa al'adar zaman kasafin kuɗi.

Sanatocin sun tafka wannan kuskuren bisa rashin sani gabanin ƙarisowar Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wanda ya gabatar da kunshin kasafin ga majalisun biyu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya isa majalisa domin gabatar da kasafin kudi, bayanai sun fito

Shugaba Tinubu ya isa zauren majalisar tare da rakiyar wasu hadimansa, ministoci da wasu gwamnoni da misalin ƙarfe 11:10 na safiyar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda Sanatocin suka tafka kuskure

A al'ada da kuma ƙa'idar majalisa, Sanataci na fara zama tsakanisu a zauren majalisarsu daga bisani su tafi a tare zuwa zauren majalisar wakilai amma ba su zuwa ɗaiɗaiku.

Sai dai wasu Sanatoci gabanin zaman na hadin gwiwa sun wuce kai tsaye zuwa zauren majalisar wakilai bisa rashin sani wanda ya daure wa ‘yan majalisar kai.

Yayin da suka fahimci gonar da suka tafka, Sanatocin da suka yi wannan kuskuren kamar Aliyu Wamakko (APC, Sokoto ta arewa) da Monday Okphebolo (APC, Edo ta tsakiya) cikin hanzari suka fito.

A lokacin da Wamakko da Okphebolo ke hanzarin komawa zauren majalisar dattawa sai suka ci karo da sauran sanatocin sun fito gaba ɗaya zasu tafi zaman haɗin guiwa.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta ɓalle a majalisar dokokin jihar Bauchi bayan hukuncin kotun ɗaukaka ƙara

Kuskuren da sanatocin biyu suka yi ya faru ne daga rashin zurfin ilimi da fahimtar ayyukan majalisa da hanyoyin gudanar da irin wannan zama na hadin gwiwa, The Nation ta ruwaito.

Tinubu ya dira majalisar tarayya

A wani rahoton kuma Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya isa majalisar tarayya domin gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2024.

Wannan shine karo na farko da Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin a gaban ƴan majalisun tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel