Yanzun nan: Shugaba Tinubu Ya Sake Naɗa Shugaban Kamfanin Man Fetur Na Kasa da Wasu Mutum 8

Yanzun nan: Shugaba Tinubu Ya Sake Naɗa Shugaban Kamfanin Man Fetur Na Kasa da Wasu Mutum 8

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da sake naɗa Malam Mele Kyari a matsayin shugaban kamfanin man fetur na ƙasa NNPCL
  • Shugaban ƙasar ya kuma naɗa majalisar gudanarwan kamfanin wadda ta ƙunshi Pius Akinyelure a matsayin shugaba
  • A sanarwan da kakakin shugaban ƙasa ya fitar ranar Litinin, ya ce naɗe-naɗen zasu fara aiki daga ranar 1 ga watan Disamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sake naɗa Malam Mele Kyari, a matsayin shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL).

Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale, ya fitar ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, 2023.

Kara karanta wannan

Murna tayin da Shugaba Tinubu ya ƙara yin muhimman naɗe-naɗe guda biyu a Gwamnati

Shugaban kasa, Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Sake Nada Mele Kyari a Matsayin Shugaban NNPCL Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

A cewar Ngelale, naɗin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Disamba, 2023, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce shugaban ya kuma nada majalisar gudanarwar kamfanin, wadda ta kunshi Cif Pius Akinyelure a matsayin shugaban majalisar gudanarwa na kamfanin NNPCL.

A rahoton da The Nation ta tattaro, sanarwan ta ce:

"Bisa la'akari da sashi na 59 (2) na dokar kamfanin man fetur 2021, shugaban kasa, Bola Tinubu, ya amince da nadin sabon kwamitin gudanarwa na kamfanin man fetur na kasa (NNPCL) daga ranar 1 ga Disamba, 2023."

Jerin naɗin da shugaba Tinubu ya yi a NNPCL

Legit Hausa ta tattaro muku jerin naɗin da shugaban kasa ya yi a kamfanin man fetur na ƙasa NNPCL, ga su kamar haka:

1. Chief Pius Akinyelure - Shugaban majalisar gudanarwa ta NNPCL

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama, ta yanke hukunci kan zaɓen gwamnan jihar Sakkwato

2. Mallam Mele Kolo Kyari - Shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL)

3. Alhaji Umar Isa Ajiya - Shugaban sashin kuɗi na kamfanin mai

4. Mista Ledum Mitee - Darakta

5. Mista Musa Tumsa - Darakta

6. Mista Ghali Muhammad - Darakta

7. Farfesa Mustapha Aliyu - Darakta

8. Mista David Ogbodo - Darakta

9. Eunice Thomas - Darakta.

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan zaben Sokoto

A wani rahoton na daban kuma Kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato a zaben 2023.

Kwamitin alkalai uku na kotun ne suka yanke wannan hukunci da murya ɗaya ranar Litinin, 27 ga watan Nuwamba, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel