Ministan Tinubu Ta Yi Wa 'Yan Najeriya Babban Albishir Kan Wutar Lantarki

Ministan Tinubu Ta Yi Wa 'Yan Najeriya Babban Albishir Kan Wutar Lantarki

  • Gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta sha alwashin kawo karshen duk wasu matsaloli da ke addabar fannin wutar lantarki
  • Gwamnatin ta ce kudurin dokar wutar lantarki na 2023 zai tabbatar da cewa 'yan Najeriya sun more ingantacciyar wutar lantarki
  • Ministan wutar lantarki Adelabu ya ce akwai tsarin da za su kaddamar da zai kawo tsayuwar wutar lantarki a birane da kauyukan Najeriya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu a ranar Alhamis, 30 ga watan Nuwamba, ya ce kudurin dokar wutar lantarki na 2023 zai inganta samar da wutar a Najeriya.

Ya sha alwashin cewa 'yan Najeriya sun kusa fara more ingantacciyar wutar lantarki a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama kan shari'ar zaben dan Majalisar PDP, ta bayyana mai nasara

Adebayo Adelabu/Wutar lantarki
Ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu ya sha alwashin cewa 'yan Najeriya sun kusa fara more ingantacciyar wutar lantarki a fadin kasar. Hoto: Vithun Khamsong
Asali: Getty Images

Ya bayyana hakan ne a taron horas da mambobin kungiyar masu samar da wutar lantarki (PICAN) karo na uku da aka gudanar a Abuja, rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muhimmancin kudurin dokar wutar lantarki na 2023 - Minista

Taken wannan taron shi ne: "Kawo karshen matsalar wutar lantarki a Najeriya: Yin amfani da kudirin dokar wutar lantarki na 2023"

Ministan ya ce ma damar aka fara aiwatar da abubuwan da ke kunshe a cikin kudurin dokar wutar, to babu inda ba za a samu wutar lantarki mai inganci a kasar ba.

A cewar sa wani sashe mai muhimmanci a cikin kudurin dokar wutar lantarki na 2023 shi ne bunkasa tsare-tsare da dabarun samar da wutar lantarki a Najeriya.

Tinubu ya ba fannin wutar lantarki muhimmanci - Minista

Adelabu ya ce:

"Akan wannan ne muke aiki da cibiyar wutar lantarki ta kasa (NCP) don yin gyara da tura wannan tsari ga majalisar zartaswar tarayya (FEC) domin sa hannu da sahalewa.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Babban Dan Siyasa, Wasu Kan Damfara Ta Naira Miliyan 607

A cewarsa, akwai tsarin da gwamnatin tarayya za ta kaddamar da ya shafi amfani da mita, rarraba kayayyakin wutar lantarki, don kawo tsayuwarta a fadin kasar.

Premium Times ta taba ruwaito Adelabu na ce kawo karshen matsalar wutar lantarki na daga cikin kudurorin gwamnatin Tinubu kamar yadda yake a jaddawalin "k undin samar da sabuwar Najeriya".

Kasafin 2024: SDP ta shirya ba Tinubu goyon baya

A wani labarin, jam'iyyar SDP ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu tare da yakinin Najeriya za ta samu ci gaba nan gaba kadan, Legit Hausa ta ruwaito.

Jam'iyyar ta kuma jinjinawa Shugaba Tinubu kan mayar da hankali wajen magance matsalolin tsaro da farfado da tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel