Shugaba Tinubu Ya Tabbatar da Naɗin Mace a Matsayin Shugabar Hukumar NIS Ta Ƙasa

Shugaba Tinubu Ya Tabbatar da Naɗin Mace a Matsayin Shugabar Hukumar NIS Ta Ƙasa

  • Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da naɗin Wura-Ola Adepoju a matsayin kwanturola Janar ta hukumar NIS ta ƙasa
  • Ƙafin wannan naɗi, Adepoju tana riƙe da matsayin mukaddashin shugaban hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS)
  • Tuni dai masu ruwa da tsaki daga Kadu maso Yamma suka jinjinawa naɗin mace ƴarsu a wannan babban matsayi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da nadin Wura-Ola Adepoju a matsayin kwanturola-janar ta Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS).

Adepoju ta bayyana hakan ne ga ma’aikatan hukumar NIS yayin faretin babban kwanturola na ƙasa ranar Laraba, 29 ga watan Nuwamba, 2023, cewar rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Wasu hadimai sun yi jabun sa hannun gwamnan APC don sace kuɗi? Gaskiya ta bayyana

Kwantura janar ta NIS, Wura-Ola Adepoju.
Shugaba Tinubu Ya Nada Mace a Matsayin Shugabar Hukumar Shige da Fice NIS Hoto: thecable
Asali: UGC

A kalamansa, Misis Adepoju ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Zaku so sanin cewa cikin ikon Allah da amincewar gwamnatin yanzu, an tabbatar da ni a matsayin babbar kwanturola-janar ta hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS)."

Ta kuma bayyana cewa nan ba da daɗewa ba za a anar da ranar bikin naɗinta a wannan babban matsayi wanda a yanzu take riƙo.

NIS ta tabbatar da naɗin CG

Mai magana da yawun hukumar NIS, Anyanwu Ifeanyi, ya tabbatar da hakan ga jaridar The Cable yayin da aka nemi jin ta bakinsa.

"Eh kwarai da gaske, an tabbatar da naɗinta a matsayin cikakkiyar kwanturola janar," in ji shi a wani saƙon da turo.

A ranar 29 ga watan Mayu aka nada Adepoju a matsayin mukaddashin CG ta NIS, inda ta maye gurbin Isah Jere wanda wa'adinsa ya kare a ranar 29 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya rantsar da mutane 8 da ya naɗa, ya shiga taro da manyan jiga-jigai a Villa

Wannan naɗi ya jima yana shan yabo

Masu ruwa da tsaki sun yaba da naɗin Adepoju, mace ta farko daga shiyyar kudu maso Yamma a matsayin muƙaddashin shugabar NIS ta ƙasa. Sun ce an kafa tarihi.

A cewarsu, wannan nadin zai zaburar da mata jami’ai su bada gagarumar gudummuwa da aiki tuƙuru yayin gudanar da ayyukansu da fatan kaiwa wani matsayi.

Kasafin kuɗin 2023 ya tsallaka gaba

A wani rahoton kuma Kasafin kuɗin shekarar 2024 wanda shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya gabatar ya tsallake zuwa karatu na biyu a majalisar wakilai.

Shugaban masu rinjaye na majalisar, Julius Ihonvbere ne ya jagoranci mahawara kan kasafin a zaman yau Alhamis, 30 ga watannNuwamba, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel