Shugaba Tinubu Ya Aike da Muhimman Saƙo Ga Majalisar Dattawa Kan Kasafin Kuɗin 2024

Shugaba Tinubu Ya Aike da Muhimman Saƙo Ga Majalisar Dattawa Kan Kasafin Kuɗin 2024

  • Bola Ahmed Tinubu ya rubuta wasiƙa zuwa majalisar dattawa kan kasafin kuɗin 2024 da zai gabatar gobe Laraba, 29 ga watan Nuwamba
  • Shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, ne ya karanta sakon shugaban ƙasan a zaman yau Talata
  • Bayan haka ne majalisar ta amince da buƙatar Bola Tinubu na yin zaman tare da mambobin majalisar wakilan tarayya a gobe Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana aniyarsa ta gabatar da kudirin kasafin kudin shekarar 2014, na farko tun bayan hawansa kan gadon mulki.

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Tinubu Ya Aike da Wasiƙa Ga Majalisar Dattawa Kan Kasafin Kuɗin 2024 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Shugaban ƙasar ya sanar da shirinsa na gabatar da kasafin kuɗin idan Allah ya kaimu ranar Laraba (gobe), 29 ga watan Nuwamba, 2023, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kwanaki 6 da dawowa Najeriya, Shugaba Tinubu zai lula kasar Larabawa gobe

Tinubu ya bayyana ranar gabatar da kudirin a zaman haɗaka na majalisar tarayya a wata wasiƙa da ya aika zuwa majalisar dattawan Najeriya ranar Talata.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ne ya karanta wasiƙar shugaban kasa a zaman sanatoci na yau 28 ga watan Nuwamba, Vanguard ta tattaro.

Majalisar dattawa ta amince da buƙatar shugaba Tinubu

Bayan haka ne, majalisar dattawan ta amince da buƙatar shugaba Tinubu na gudanar da zaman haɗaka da takwaorinsu na majalisar wakilai ranar Laraba.

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan majalisar tarayya ta hannun sakataren yaɗa labarai, Dakta Ali Barde Umaru, ta sanar da cewa Bola Tinubu zai gabatar da jawabi ranar 29 ga watan Nuwamba.

Wannan ne karo na farko da shugaban ƙasar zai haɗa majalisun biyu a zama ɗaya kana ya gabatar da kasafin kudi tun bayan rantsar da shi a watan Mayu.

Kara karanta wannan

An bankado sabon shirin tayar da hargitsi a jihar Kano kan hukuncin tsige Gwamna Abba

Legit Hausa ta fahimci cewa shugaba Tinubu ya ƙara kasafin 2023 da ke dab da karewa, wanda ya ce za a yi amfani da kuɗin wajen tallafawa yan ƙasa su rage raɗaɗi.

Rikicin Shugabanci Ya Barke a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi

A wani rahoton Hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ya haddasa sabon rikicin shugabnci a majalisar dokokin jihar Bauchi ranar Talata.

Kotun ta tsige kakakin majalisar da mataimakinsa, ta umarci INEC ta shirya sabon zabe a wasu rumfunan mazaɓu biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262