Gobara Ta Tashi a Sakariyar Gwamnatin Tarayya, Bayanai Sun Fito

Gobara Ta Tashi a Sakariyar Gwamnatin Tarayya, Bayanai Sun Fito

  • An samu tashin gobara a sakatariyar gwamnatin tarayya da ke a babban birnin tarayya Abuja
  • Gobarar wacce ta tashi da misalin ƙarfe na ranar Asabar ta ƙone wasu ofisoshi na sakatariyar ciki har da na mai ba shugaban ƙasa shawara kan SDG
  • Jami'an hukumar kashe gobara ta birnin tarayya Abuja da haɗin gwiwar gwamnatin tarayya sun samu nasarar shawo kan gobarar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Gobara ta ƙone ofishin mai bawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara a kan muradun cigaba mai ɗorewa (SDG).

Daraktan sadarwa na ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya (OHCSF), Mallam Mohammmed Ahmed, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar a daren ranar Asabar, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

An tafka asara yayin da mummunar gobara ta tashi a rukunin wasu shaguna

Gobara ta tashi a sakatariyar gwamnatin tarayya
Gobara ta tashi a sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja (ba inda lamarin ya auku ba) Hoto: @dailytrust
Asali: Twitter

Menene ya haddasa tashin gobarar?

Ya ce gobarar ta shafi ɗakunan da ke hawa na biyu zuwa na takwas na sakatariyar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A kalamansa:

"Da misalin ƙarfe 2:30 na ranar Asabar an samu tashin gobara a Block C na sakatariyar gwamnatin tarayya, Phase II, Abuja."
"Gobarar ta tashi sakamakon fashewar wani abu a ɗakin kula da wutar lantarki a hawa na uku na Block C wanda mai bawa shugaban ƙasa shawara kan cigaba mai ɗorewa (SDG) ke amfani da shi a matsayin ɗakin ajiyar kayayyakin wutar lantarki mai amfani da hasken rana."
"Lamarin wanda aka shawo kansa a haɗin gwiwa tsakanin jami’an gwamnatin tarayya da hukumar kashe gobara ta FCT da misalin ƙarfe 5:00 na yamma, ya shafi ɗakunan ajiye-ajiye da ke hawa na biyu zuwa na takwas na ginin."

Kara karanta wannan

Wasu hadimai sun yi jabun sa hannun gwamnan APC don sace kuɗi? Gaskiya ta bayyana

Ya ƙara da cewa manyan sakatarori na ofishin Common Services-OHCSF, Misis Lydia S. Jafiya da ofishin ayyuka na musamman, Injiniya Faruk Yusuf Yabo da daraktoci na MDAs da abin ya shafa suna wajen, yayin da aka ci gaba da aikin shawo kan gobarar.

Gobara Ta Tashi a ABU

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin gobara a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria a jihar Kaduna.

Gobarar ta tashi a ginin da ke ɗauke da ofisoshin shugabanni da ma'aikatan jami'ar wanda yake da hawa takwas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel