Aikin Gwamnatin Najeriya
Gwamnatin tarayya za ta hada kai da jihohi domin daukan matasa aiki saboda tsaron dazukan Najeriya. Za a ba mataan horo da kayan fada domn yakar yan ta'adda.
Gwamnatin tarayya za ta nuna wasu muhimman ayyukan da Bola Tinubu ya yi a birnin London. Ministan Abuja, Nyesom Wike na cikin jami'an da za su je taron.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya dauki matakan ci gaban ilimi da suka hada da daukar jami’an tsaro 17,600, kaddamar da shirin ICT, da rancen kudin sayen mota ga malamai.
Shugaba Bola Tinubu ya jinjina wa Soludo bisa ci gaban Anambra tare da bayyana shirin yin aiki tare da gwamnan domin mayar da jihar cibiyar cigaba.
An tsaurara tsaro a Anambra gabanin ziyarar Tinubu. Ana sa ran shugaban kasar zai ƙaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamnatin jihar ta kammala.
Gwamnatin Kano ta kare kanta kan cece-kuce a kan N670m da aka ware don gyara da saya wa Sarki Sanusi II motoci, tana mai cewa ba sabon abu ba ne.
Masanin tattalin arziki, Farfesa Pat Utomi, ya ƙaddamar da gwamnatin sa ido a Najeriya. Sai dai ministan yada labarai ya ce hakan kuskure ne domin ya saba wa doka.
Shugaba Bola Tinubu ya ce matsalolin tattalin arziki sun kusan sa ya daina karanta jaridu; amma yanzu an fara ganin alfanun matakan da ya dauka kan tattalin arziki.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya gano yara suna bacci a titi da dare, ya gano iyayensu, ya tallafa musu da abinci, kuɗi da kuma ɗaukar nauyin karatunsu baki ɗaya.
Aikin Gwamnatin Najeriya
Samu kari