Dangote Ya Fadi Dalolin da Kamfaninsa zai Samu daga Fitar da Takin Zamani a Kullum

Dangote Ya Fadi Dalolin da Kamfaninsa zai Samu daga Fitar da Takin Zamani a Kullum

  • Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa kamfaninsa zai rika samun N11bn a kowace daga fitar da takin zamani cikin shekaru biyu masu zuwa
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da ake ƙoƙarin inganta hadin guiwa don samun damar fitar da kayayyakin Dangote zuwa ƙasashen waje
  • Dangote ya ce kamfaninsa ne babban abokin kasuwancin NPA, kuma nasarar ayyukansu na dogara ne da goyon bayan gwamnati

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Shugaban Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa cikin shekaru biyu masu zuwa, kamfaninsa zai rika samun kudin shiga na $7m a kullum.

Wannan adadi ya yi daidai da Naira biliyan 11 a kowace rana da kamfanin zai rika samu daga fitar da takin zamani zuwa kasashen waje.

Dangote
Kamfanin Dangote zai rika fitar da taki Hoto: Dangote Industries
Asali: Facebook

Daily Trust ta ruwaito hakan na zuwa ne a lokacin da Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA) ke hada gwiwa da Kamfanin Dangote don fadada harkokin fitar da kaya daga Najeriya zuwa kasashen waje.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar NPA ta ce tun lokacin da aka fara tsarin sayar da danyen mai a Naira a watan Oktoban 2024, jiragen ruwa guda 57 mallakar Kamfanin Dangote take kula da su duk wata.

Dangote ne babban abokin kasuwancin NPA

Trust Radio, yayin wata ziyara da ya kai hedikwatar hukumar NPA a Legas, Dangote ya fadi muhimmancin inganta mu’amala tsakanin bangarorin biyu.

Aliko Dangote, wanda shi ne mutum mafi arziki a nahiyar Afrika, ya ce:

“Mun zo ne domin mika godiya ga NPA saboda irin kyakkyawan aikin da suke yi. Domin a halin yanzu, mu ne manyan abokan ciniki na NPA.”
“Ina ganin irin wannan hadin gwiwa tsakaninmu yana da matukar muhimmanci wajen bunkasa masana’antu. Mun tattauna batutuwa da dama, ciki har da yadda za a inganta tattalin arzikin teku. Mun kuma amince da aiki tare domin amfanin Najeriya.”

Dangote ya yi karin bayani kan kamfaninsa

Alhaji Aliko Dangote ya ce girman ayyukan kamfaninsa da ke Lekki kadai zai hada da jigilar gangar danyen mai har zuwa jiragen ruwa 240.

Ya ce kowanne jirgi na dauke da gangar mai miliyan daya, kuma za a fitar da samfuran man da za su kai kusan jiragen ruwa 600 a shekara.

Dangote
Dangote ya nemi tallafin hukumar NPA Hoto: Dangote Industries
Asali: Getty Images

Ya ce:

“Za mu kuma rika fitar da takin zamani da zai kai kimanin jiragen ruwa takwas. Wannan irin aiki ba a taba ganin irinsa a kasar nan ba. Saboda haka babban kalubale ne. Amma da shugabancin da NPA ke da shi, muna da kwarin guiwar za su iya cimma wannan burin.”

Neja: Dangote zai gina kamfanin shinkafa

A wani labarin, kun ji cewa Kamfanin Alhaji Aliko Dangote tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar Neja sun sanar da fara aikin gina kamfanin sarrafa shinkafa a jihar.

An bayyana hakan ne a wani taron da aka gudanar a jihar, inda kamfanin Dangote ya ce an kammala shirye-shiryen fara aikin a tsakanin Wushishi da Bida.

Gwamnatin jihar Neja ce ta ware filin noma mai girman hekta 50 domin gina kamfanin, tare da tabbatar da bin doka da oda wajen mallakar filin don inganta noma.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.