Zaben Najeriya
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan takarar da za su fafata a dukkan matakai da su garzaya kotu idan basu gamsu da sakamakon zaben hukumar INEC ba.
A ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023 ne ake fatan yin zaben shugaban kasa da na yan majalisar tarayya a Najeriya, da bvas za a tantance masu zabe.
Za a ji yadda Gwamna yake kamfen zama Sanata a jihar Taraba da maggi da shinkafa. Wasu mutane su na zargin Darius Ishaku da gaza tabuka abin kirki a shekaru 8.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya samu wani gagarumin tagomashi a birnin tarayya Abuja. Magoya bayan PDP da LP sun koma APC.
Gabannin babban zaben shugaban kasa na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu, manyan jiga-jigan jam'iyyar PDP sun nuna yakinin cewa Atiku Abubakar zai ci zabe.
Shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa, Abdullahi Adamu, ya bayyana cewa jam'iyyar zata yi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na ranar Asabar. Yace APC tayi aiki tuƙuru.
Yan kwanaki kafin babban zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, kungiyar malaman jihar Kano sun ayyana goyon bayansu ga takarar Atiku Abubakar.
Bayan an sauya kudi, Shugaban EFCC ya tono makarkashiyar da ake yi. Baya ga kaya, Abdulrasheed Bawa ya ce akwai sababbin kudin da sai ranar zabe za a fito da su
Wata kotun majisatre ta tsare dan Majalisar Tarayya daga Jam’iyyar APC Ephraim Nwuzi, kwana biyu kafin zaben da yake neman yin tazarce a kujerar a zaben 2023.
Zaben Najeriya
Samu kari