Magoyan Bayan Jam'iyyar APC Sun Dira Ofishin Hukumar INEC a Jihar Kano

Magoyan Bayan Jam'iyyar APC Sun Dira Ofishin Hukumar INEC a Jihar Kano

  • Magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano, sun taru a gaban ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC)
  • Magoyan jam'iyyar ta APC na zanga-zanga ne domin nuna adawa da bayyana Abba Kabir Yusuf Matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar
  • Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya samu nasarar kayar da Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar

Jihar Kano- Magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun yi tururuwa zuwa ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a jihar Kano domin yin zanga-zanga kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar.

Magoya bayan jam'iyyar ta APC na zanga-zangar ne kan bayyana Abba Kabir Yusuf, ɗan takarar jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Kano da hukumar zaɓen tayi. Rahoton Daily Trust

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Gawuna Yayi Magana Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Kano, Ya Bayyana Abinda Yakamata INEC Tayi

Kanon
Magoyan Bayan Jam'iyyar APC Sun Dira Ofishin Hukumar INEC a Jihar Kano Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Masu zanga-zangar sun fito kan tituna suna ɗauke da alluna masu rubutu daban-daban a jikin su, yayin da suke rera waƙoƙi daban-daban.

Wasu waɗanda ake zargin ƴan dabam ne sun so suyi amfani da wannan damar wajen aikata ba daidai ba inda suka tilasta ƴan kasuwa kulle shagunan su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kabir Yusuf, wanda aka fi yiwa laƙabi da Gida-Gida yayi takara a zaɓen a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP).

Ɗan takarar ya samu nasarar lashe ƙuri'u 1,019,602 inda ya zarce abokin takarar sa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Nasir Gawuwa, wanda ya zo na biyu da ƙuri'a 890,705.

A nata ɓangaren jam'iyyar APC tayi watsi da sakamakon zaɓen inda ta buƙaci INEC da ta bayyana shi a matsayin wanda bai kammalu ba. Rahoton The Cable

An Shiga Zullumi Bayan INEC Ta Ki Amincewa Da Sakamakon Zaben Jihohi 2, Ta Bayyana Dalili

Kara karanta wannan

Da Sake: Dan Takarar Gwamnan APC Yayi Fatali Da Sakamakon Zabe, Yasha Wani Babban Alwashi

A wani labarin na daban kuma, an shiga zaman zullumi bayan hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa, ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen gwamnonin jihohi biyu, da aka gudanar ranar Asabar, 18 ga watan Mayun 2023.

Hukumar ta INEC ta bayyana cewa ta ƙi amincewa da sakamakon zaɓen waɗannan jihohin 2 ne saboda kurakuran da aka tafka a ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel