Abba Gida-Gida: Sarakunan Kano Da Gaya Sun Taya Zababben Gwamnan Kano Murna, Sun Bashi Shawara

Abba Gida-Gida: Sarakunan Kano Da Gaya Sun Taya Zababben Gwamnan Kano Murna, Sun Bashi Shawara

  • Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya zababben gwamnan jihar Kano murnar cin zabe
  • Shima mai martaba Sarkin Gaya, Alhaji Ibrahim Gaya, ya mika sakon taya murna da fatan alheri ga Abba Kabir Yusuf
  • Sarakunan biyu sun shawarci Abba Kabir Yusuf ya hada kai da al'umma domin kawo cigaba da inganta tattalin arzikin jihar Kano

Kano - Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Gaya, sun taya zababben gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, murna kan nasararsa a zaben ranar Asabar.

A cikin wata wasika ga zababben gwamnan, Bayero ya ce mutanen Kano sun yi na'am da tsarin dimokradiyya.

Abba Kabir Yusuf
Sarakunan Kano Da Gaya Sun Taya Zababben Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Murnar Cin Zabe. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida Ya Umurci Masu Tattaki Zuwa Kano Taya Shi Murna Su Dakata, Ya Fadi Abu 1 Da Ya Ke Son Su Mishi

Ya ce za a iya ganin hakan ta yadda suka fito kwansu da kwarkwata suka kada kuri'unsu, Daily Trust ta rahoto.

Sarkin Kano ya yi wa Abba Kabir Yusuf Fatan Alheri

Sarki Bayero ya kuma mika godiya ga malaman addinin musulunci, limamai da sauran mutanen gari saboda addu'a da suka yi kafin, yayin da bayan zabe.

Ya kuma yi kira ga zababben gwamnan ya hada kai da al'umma wurin tafiyar da gwamnatinsa, saboda yin hakan zai inganta rayuwan mutane da tattalin arziki.

Ya kuma yi addu'ar saman zaman lafiya mai dorewa a Kano da sauran sassan kasar yayin da ya yi addu'a ga Allah ya bawa zababben gwamnan nasarar kammala wa'adinsa lafiya da kawo cigaba a jihar.

Sakon Sarkin Gaya ga Abba Kabir Yusuf, zababben gwamnan Kano

A bangarensa, Sarkin Gaya, Aliyu Ibrahim Gaya, shima ya taya zababben gwamnan murna, ya bayyana fatan alheri.

Wasikar ta ce:

Kara karanta wannan

Gwamna Ya Taya Tinubu Murna Bayan Kwana 21, Ya Nemi Bukata 1 a Gwamnatinsa

"Muna da kwarin gwiwa cewa mai girma zai kawo cigaba ga jihar da kasa baki daya. Idan aka yi la'akari ga kwarewarka, wayewa da halin jagoranci, wannan zai zama abu mai sauki. Mun taru da abokan arziki da muna maka fatan Allah ya maka jagora, ya kare ka ya kuma saukaka maka."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel