Yadda Abokai Na Suka Ci Amanata a Zaben Gwamna, Gwamna Dapo Abiodun

Yadda Abokai Na Suka Ci Amanata a Zaben Gwamna, Gwamna Dapo Abiodun

  • Gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya koka kan yadda mutanen da ya aminta da su suka ci amanar sa lokacin zaɓe
  • Gwamnan na jam'iyyar APC yace mutanen da yake ganin na kusa da shi ne sun ci masa dundunniya a lokacin zaɓen gwamnan jihar
  • Gwamna Abiodun ya sha da ƙyar a zaɓen gwamnan jihar inda tazarar da ya ba abokin takarar sa ba wata mai yawa bace

Jihar Ogun- Gwamnan jihar Ogun. Dapo Abiodun ya koka kan yadda na kusa da shi suka ci amanar sa a lokacin zaɓen gwamnoni da aka kammala.

Hukumar INEC a ranar Lahadi ta bayyana Abiodun a matsayin wanda ya lashe zaben jihar inda ya samu ƙuri'u 276,298, yayin da Ladi Adebutu na jam'iyyar PDP ya zo na biyu inda ya samu ƙuri'u 262,383. Rahoton Daily Trust

Kara karanta wannan

Tazarce: Gwamna Zulum Da Jerin Sauran Gwamnonin Da Zasu Sake Shan Jar Miya Ya Zuwa Yanzu

Abiodun
Yadda Abokai Na Suka Ci Amanata a Zaben Gwamna, Gwamna Dapo Abiodun Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Abiodun yayi rashin nasara a mafi yawancin ƙananan hukumomin dake shiyyar Ogun ta Gabas, shiyyar da ya fito ciki har da ƙaramar hukumar sa Ikenne.

A ranar Talata, gwamna Abiodun ya kai ziyara mahaifar sa ta Iperu-Remo, inda mutanen garin da magoya bayan jam'iyyar APC suka fito domin tarbar sa. Rahoton Within Nigeria

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da yake magana a wajen da aka tarbe shi, Abiodun yace nasarar ta samu ne a dalilin ubangiji da kuma goyon bayan da mutane suka nuna masa a lokacin zaɓe.

A kalamansa:

“Wannan zaɓen ya nuna cewa ɗan adam bai sauya hali sannan Allah ne kaɗai abin dogaro. A yayin wannan zaɓen, mutanen da mu kayi tunanin abokan mu ne sun ci amanar mu, mutane sun ci mana dundunniya, sannan da yawa sun bamu kunya.
“Ina sane da cewa har waɗanda suke kiran kan su a matsayin abokan mu, ba su zaɓe mu ba, amma wannan ba komai bane yanzu tunda anyi zaɓe an gama sannan Allah ya bamu nasara."

Kara karanta wannan

Zaben Gwamnan Katsina: PDP Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Bayan Shan Kaye

“Amma bai kamata muyi mamaki ba saboda ko a Bible, an ci amanar Yesu Almasihu duk da irin abubuwa masu kyau da yayi. Dole ne mu godewa Allah saboda duk da irin cin amanar da aka yi mana, ya sanya mun samu nasara."

Duk da Guguwar Peter Obi, Jam’iyyar LP Ta Gaza Samun Gwamna ko 1 a Zaben Jihohi

A wani labarin na daban kuma, rahoto ya zo kan yadda har yanzu jam'iyyar Labour Party (LP) ta gaza samun kujerar gwamna ko ɗaya a zaɓen jihohi.

A baya an yi tunanin guguwar Peter Obi za ta sanya jam'iyyar ta.karɓe mulkin wasu jihohi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel