Gwamnan Bauchi Ya Shirya Yin Sulhu Da Masu Adawa Da Shi

Gwamnan Bauchi Ya Shirya Yin Sulhu Da Masu Adawa Da Shi

  • Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya aike da wani sabon albishir ga abokan adawar sa na ciki da wajen jam'iyyar PDP
  • Gwamna Bala Mohammed yace duk wasu masu son ganin bayan sa, su kwantar da hankulan su domin ya yafe musu
  • Gwamnan ya kuma ce a shirye yake yaga duk wasu masu adawa da shi ya daidaita tsakanin su

Jihar Bauchi- Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana cewa ya yafewa waɗanda suka so ganin bayan sa a ciki da wajen jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), bayan ya samu nasarar sake komawa kan kujerar sa.

Gwamna Bala Mohammed, ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels Tv a shirin su na Siyasa a Yau.

Bala Mohammed
Gwamnan Bauchi Ya Shirya Yin Sulhu Da Masu Adawa Da Shi Hoto: Premium Times
Asali: Twitter

Gwamnan ya kuma bayar da tabbacin cewa a shirye yake ya sulhunta da duk wasu masu jin haushin sa.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Ba Zan Taba Zama Dan APC Ba, Inji Fayose

A cewar sa har yanzu akwai sarakunan gargajiya da malamai waɗanda suka haɗa kai da abokan hamayyar sa na siyasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na yafe musu. Abinda nake so yanzu shine in ga na haɗa kawunan kowa." Inji shi

Sai dai gwamnan yace babu wani ɗan jam'iyyar PDP a jihar da yaci dunduniyar sa da sauran jiga-jigan jam'iyyar.

"Mutane irin su tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayya dama can ba tare su ke da mu ba. Tsohon gwamnan Bauchi, Adami Muazu, kawai ɗan takarar shugaban ƙasar mu yake so."
“Dama can tun asali abokin hamayya ta ne sannan na sha ba shi haƙura bisa kayen da nayi masa a shekarar 2007. Nayi zaton an manta da wannan, amma har yanzu ya kasa haƙura."
“Sauran ɗayan dattijon kuma, mahaifina Waziri (Muhammadu Bello Kirfi), wanda ya so yayi amfani da masarauta wajen yaƙa ta sannan aka tuɓe shi kuma ya dawo yana jin ɗora alhakin hakan a kai na, na aminta lokacin cire shi ne yayi."

Kara karanta wannan

Sun Ki Allah Ya Nufa: Yadda Na Kusa Da Ni Suka Ci Amanata a Lokacin Zabe, Gwamnan APC Yayi Bayani Mai Sosa Rai

Amma gwamnan yace a iya sanin sa, ya san cewa Kirfi bai taɓa zama mamban wata jam'iyya ba.

Gwamnan ya kuma bayyana cewa yana da niyyar ganin ya ɗinke duk wata ɓaraka da take a cikin jam'iyyar PDP a jihar.

Buhari Ya Yi Alfahari, Ya Bayyana Yadda Ya Hana Siyan Kuri'a A Zaben 2023

A wani labarin na daban kuma, shugaba Buhari ya bigi ƙirji ya bayyana yadda ya hana siyan ƙuri'a a zaɓen 2023.

A ranar Asabar da ta gabata ne aka kammala manyan zaɓuka a tarayyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel