Masu Zanga-Zanga Na Neman Shugaban INEC Yayi Murabus Daga Kujerar Sa

Masu Zanga-Zanga Na Neman Shugaban INEC Yayi Murabus Daga Kujerar Sa

  • Masu zanga-zanga sun taso shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa a gaba kan sai yayi murabus
  • Masu zanga-zangar na neman farfasa Mahmood Yakubu yayi murabus daga kujerar sa kan rikicin da aka samu lokacim zaɓe
  • A cewar su a lokacin zaɓen an tauye haƙƙin ƴan Najeriya da dama ta hanyar hana su kaɗa ƙuri'un su

Abuja- Masu zanga-zanga daga jihohi daban-daban na tarayyar Najeriya a ranar Alhamis sun dira birnin tarayya Abuja suna neman shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) yayi murabus.

Masu zanga-zangar suna neman farfesa Mahmood Yakubu yayi murabus daga kan muƙamin sa saboda rikicin da aka samu a zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairun 2023. Rahoton Daily Trust

Yakubu
Masu Zanga-Zanga Na Neman Shugaban INEC Yayi Murabus Daga Kujerar Sa
Asali: Original

Idan ba a manta ba dai an samu rikici, kwacen takardun kaɗa ƙuri'a da akwatunan zaɓe, da harbe-harbe a wasu jihohi a lokacin zaɓen.

Shugaban masu zanga-zangar, Anngu Orngu, yace wasu matasa da suka fito a karon su na farko domin kaɗa ƙuri'un su, an hana su yin zaɓen a dalilin rikicin da ya auku a zaɓen.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A kalamansa:

“Mu ƴan Najeriya ne mara sa son tashin hankali, amma zamu yi amfani da duk hanyar da ta dace bisa doka wajen ganin cewa an biya mana buƙatun mu."
"Mun taru a nan ne cikin takaici domin an tattaka ƴancin da ƴan Najeriya suke da shi, sannan mun taru a nan ne domin yin kira kan yin murabus ɗin shugaban hukumar INEC, farfesa Mahmood Yakubu da gaggawa."

Wani jagoran zanga-zangar a ƙarƙashin ƙungiyar National Youth League for the Defence of Democracy (NYLDD), Dr Moses Paul, ya bayyana cewa:

“An ƙona mutane a Kano, an harbi mutane a Rivers, mun ga rashin imanin da aka yi a jihar Legas duk a lokacin zaɓen nan."

Jaridar Tribune ta rahoto cewa masu zanga-zangar na kuma neman shugaba Buhari da ya kafa gwamnatin riƙon ƙwarya kafin ƙarewar wa'adin mulkin sa.

Kotun Daukaka Kara Zata Zartar Da Hukunci Kan Shari'ar Gwamnan Jihar Osun

A wani labarin na daban kuma, kotun ɗaukaka ƙara ta shirya zartar da hukuncin ta kan sahihin gwamnan jihar Osun.

Kotun ɗaukaka ƙarar za ta yi hukuncin ta ne a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel