Takarar Shugabancin Majalisar Dattawa Ta Kara Dumi, Sanatoci Da Dama Na Son Gaje Ahmad Lawan

Takarar Shugabancin Majalisar Dattawa Ta Kara Dumi, Sanatoci Da Dama Na Son Gaje Ahmad Lawan

  • Masu neman gaje kujerar shugabancin majalisar dattawa daga hannun Ahmad Lawan na ta ƙara yawa
  • Ya zuwa yanzu manyan sanatoci bakwai sun bayyana aniyar su ta neman kujerar shugabancin majalisar dattawan ta 10
  • Wasu daga cikin manya-manyan sanatocin dake kan gaba sun haɗa da, Orji Uzor Kalu, Sanata Mohammed Ali Ndume, Sanata Godswill Akpabio da sauran su

Abuja- Ya zuwa yanzu akwai sama da sanatoci biyar daga yankuna biyar na ƙasar nan dake shirin faftawa domin neman shugabancin majalisar dattawa ta 10. Rahoton The Nation

Waɗannan sanatocin dai tsaffin hannu ne domin sun san duk wata kitimurmura da ake ƙullawa a fagen siyasar Najeriya, kuma a shirye suke da su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun samu wannan kujerar mai tsoka.

Dattawa
Takarar Shugabancin Majalisar Dattawa Ta Kara Dumi, Sanatoci Da Dama Na Son Gaje Ahmad Lawan Hoto: The Nation
Asali: UGC

Sannan kuma, dukkanin masu neman shugabancin majalisar dattawan ta 10 sun fito ne daga jam'iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yanzu: Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Ekweremadu Bisa Zargin Safarar Sassan Jiki

Uku daga cikin manyan sanatocin dake kan gaba sun haɗa da; Barau Jibrin (Kano ta Arewa, Arewa maso Yamma); Orji Uzor Kalu (Abia ta Arewa, Kudu maso Gabas) da David Umahi (Ebonyi ta Kudu, Kudu maso Gabas). Rahoton The Punch

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Waɗannan sanatocin uku sune waɗanda suka fito fili suka bayyana aniyar su ta neman shugabancin majalisar dattawan Najeriya ta 10.

Sauran sanatocin dake neman shugabancin majalisar sune shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan (Yobe ta Arewa, Arewa maso Gabas), Mohammed Sani Musa (Niger ta Gabas, Arewa ta Tsakiya), Mohammed Ali Ndume (Borno ta Kudu, Arewa maso Gabas) da Godswill Akpabio (Akwa Ibom, Kudu maso Kudu).

A satin da ya gabata shugaban jam'iyyar APC na ƙasa ya nemi masu neman shugabancin majalisar da su jira tsarin karɓa-karɓa da jam'iyyar zata fito da shi kan majalisar.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: DSS Ta Damƙe Ɗan Majalisa Kan Hannu a Laifin da Ya Shafi Karancin Naira

Da yake bayyana aniyar sa ta zama shugaban majalisar dattawan, Kalu yace yanzu lokacin shi yayi da yakamata ya shugabanci majalisar.

Sanata Jibrin Barau Maliya lokacin da ya bayyanawa duniya kuɗirin sa na neman shugabancin majalisar yace yana takarar ne saboda duk ya fi sauran ƴan takarar cancanta.

Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, wanda wannan ne karon sa na farko a majalisar, yace idan jam'iyyar APC ta kai shugabancin majalisar yankin Kudu maso Kudu, to a shirye yake ya nemi shugabancin majalisar domin yana da ƙwarewa.

Sai dai akwai masu ganin cewa yakamata jam'iyyar APC ta miƙa ragamar shugabancin majalisar ga wani yanki ba tare da anyi takara ba.

A ranar 13 ga watan Yunin 2023 za a ƙaddamar da sabuwar majalisar dattawan ta 10 bayan shugaban ya sanar da shelantar da hakan.

Jerin Jiga-Jigan 'Yan siyasa 8 da Suka Tafka Asara Goma da Ashirin a Zaben Najeriya

A wani labarin na daban kuma, rahoto ya zo kan ƴan siyasar da suka yi biyu babu suka tafka asara a babban zaɓen da aka gudanar a faɗin tarayyar Najeriya.

Waɗannan ƴan siyasa dai zaɓen wannan shekarar bai yi musu da kyau ba inda suka yi biyu-biyu ba su tashi da komai ba, sai dai asara da ta gitta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel