Atiku Ya Garzaya Kotu, Ya Lissafo Hanyoyi 12 Da INEC Ta Taimaki Tinubu Ya Kayar Da Shi

Atiku Ya Garzaya Kotu, Ya Lissafo Hanyoyi 12 Da INEC Ta Taimaki Tinubu Ya Kayar Da Shi

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya garzaya kotu neman haƙƙin sa
  • Atiku Abubakar a ƙarar da ya shigar, ya lissafo wasu laifuka 12 da INEC tayi da suka taimaka Tinubu yayi nasara a zaɓen
  • Ɗan takarar na jam'iyyar PDP yaje gaban kotun da wasu buƙatun sa guda biyu da yake neman ta biya masa

Abuja- Ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya lissafo wasu laifuka 12 da yake zargin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) tayi waɗanda suka taimakawa Tinubu samun nasara.

Bola Tinubu, zaɓaɓɓen shugaban ƙasa kuma ɗan takarar jam'iyyar All Progressives Congress (APC), a zaɓen shugaban ƙasa, yayi nasara akan Atiku a zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Abubakar
Atiku Ya Garzaya Kotu, Ya Lissafo Hanyoyi 12 Da INEC Ta Taimaki Tinubu Ya Kayar Da Shi Hoto: Premium Times
Asali: UGC

A wata ƙara da Atiku ya shigar gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa, wacce ke zamanta a Abuja, ɗan takarar da jam'iyyar sa ta PDP suna neman a ƙwace nasarar da Tinubu ya samu. Rahoton Premium Times

Kara karanta wannan

“Karku Rantsar da Tinubu Domin Yin Hakan Ya Sabawa Dokar Tsarin Mulkin Najeriya” - Baba Ahmed

Atiku da PDP a cikin koken da suka shigar ranar Talata, sun haƙiƙance cewa nasarar Tinubu bata inganta saboda wuru-wurun da akayi a zaɓen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake lissafo laifukan zaɓen da ake zargin INEC da su, Atiku ya zargi INEC da tauye ƙuri'u, maguɗin ƙuri'a da akwatin zaɓe, maguɗi a na'urar BVAS, maguɗi wajen tantancewa da tattara sakamako, magudi wajen kai kayayyakin zaɓe.

Sauran laifukan sun haɗa da, maguɗin kayayyakin zaɓe, tsoratar da masu zaɓe, dangwale ƙuri'u da lalata kayan zaɓe, ƙwace kayayyakin zaɓe, lalatawa da yin rubutu fiye da ƙa'ida, shigar da sakamakon da ba shine a takardun rubuta sakamakon zaɓe.

A cikin ƙarar wacce lauyoyin Atiku suka shigar ƙarƙashin jagorancin Joe-Kyari Gadzama (SAN), yayi zargin cewa INEC ta ƙi yin amfani da tanadin sabuwar dokar zaɓe ba da kundin tsarin mulkin Najeriya wajen gudanar da zaɓen shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Da Sake: Dan Takarar Gwamnan APC Yayi Fatali Da Sakamakon Zabe, Yasha Wani Babban Alwashi

Atiku Abubakar ya buƙaci kotun da ta bayyana shi a matsayin shugaban ƙasa ko kuma ta sanya a sake sabon zaɓe. Rahoton Thisday

Daga Karshe Gawuna Yayi Magana Kan Sakamakon Zaben Gwamnan Jihar Kano

A wani labarin na daban kuma, Nasiru Gawuna, ɗan takarar gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin inuwar jam'iyyar APC yayi magana kan sakamakon zaɓen gwamnan jihar.

Gawuna yace INEC tayi kuskure inda ya bayyana abinda yakamata ace hukumar zaɓen tayi game da zaɓen gwamnan Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel