Abba Gida-Gida Ya Umurci Masu Tattaki Zuwa Kano Taya Shi Murna Su Dakata, Ya Fadi Abu 1 Da Ya Ke Son Su Mishi

Abba Gida-Gida Ya Umurci Masu Tattaki Zuwa Kano Taya Shi Murna Su Dakata, Ya Fadi Abu 1 Da Ya Ke Son Su Mishi

  • Zababben gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf ya roki ma su tattaki don taya shi murnar lashe zabe da su dakata, su yi masa addua maimakon haka
  • Abba, ta bakin mai magana da yawun sa, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ce idan aka yi la'akari da irin matsalar tsaron da ke addabar kasar nan, tattakin ba shi da amfani
  • Abba ya yi alwashin gudanar da gwamnatin da za ta kula rayuwar kowa ta yadda za a amfani dimukradiyya

Jihar Kano - Zababben gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da aka fi sani da Abba Gida Gida, ya roki masu tattaki a kafa daga sassan kasar nan zuwa Kano don taya shi murna da su dakata.

Maimakon haka, ya bukaci da su taya shi da addu'ar Allah ya taya shi riko don gudanar da mulki cikin adalci yadda kowa ya kurbi romon dimukradiyya, Daily Trust ta rahoto.

Abba Kabir
Abba Kabir Yusuf ya umurci masu tattaki zuwa taya shi murna a Kano su dakata. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wasu kafafen sada zumunta sun ruwaito cewa wani matashi ya fara tattaki daga Suleja a Jihar Niger don taya zababben gwamnan Kano murna.

Masu tattaki zuwa taya ni murna a Kano su dakata, su yi min addu'a, Abba Kabir Yusuf

Amma Abba a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba ta hannun mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya ce addu'a ta isa ta nuna irin goyon baya da taya shi murnar nasarar da ya yi maimakon tattaki mai nisa, musamman in aka yi la'akari da yanayin rashin tsaro da ake fama da shi a kasar.

Ya ce:

''Muna godiya ga magoya baya a ciki da wajen Jihar Kano, zababben gwamnan ya roki ma su tattaki da su dakatar da tattakin saboda ba lallai hakan ya taimaka wajen kawo karshen matsalar tattalin arziki da kalubalen da ke tunkarar gwamnati mai jiran gado bayan karbar mulki ranar 29 ga watan Mayu, 2023.

''Gwamnan Jihar Kano mai jiran gado ya ce zai fi mayar da hankali kan cigaban Kano ta hanyar inganta tsaro, lafiya, ilimi, tattalin arziki, tsara birane da kauyuka da kuma jindadin dattijai, ma'aikatan gwamnati da kuma masana'antu a matsayin taken gwamnatin Abba.
''A matsayina na gwamnan al'ummar Kano, Injiniya Abba ya bukaci kowa ya bayar da gudunmawa don tabbatar da tafiya karkashin tsarin Kwankwasiyya da kuma jam'iyyar NNPP don tabbatar da cigaban da zai taimaki kowa a fadin jihar."

Gwamnan Samuel Ortom Ya Sha Kaye Zaben Sanata, Dan Takarar APC Ya Lashe Zaben

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ya sha kaye a zaben sanata na mazabar Benue North West da aka yi a ranar 23 ga watan Fabrairu inda dan takarar APC, Cif Titus Zam ya ci zaben.

Asali: Legit.ng

Online view pixel