Zaben Najeriya
Kakakin majalisar tarayya, Tajudeen Abbas ya rantsar da 12 daga cikin zababbun mambobi 15 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gabatar a ranar Laraba.
Majalisar wakilan tarayya ta amince da kudirin garambawul ga kundin dokokin zaben Najeriya, a yanzu ya tsallake karatu na farko ya shiga na biyu yau Laraba.
APC, PDP da sauran jam'iyyu sun goge raini a jihohin da aka yi zaben cike gurbi. Jam’iyyar APC ta fi kowa tashi da kujeru masu yawa da aka gudanar a makon jiya.
Yadda aka raba ragowar kujerun majalisa tsakanin PDP da APC a Kaduna. A kusan duka zabukan da aka shirya, jam'iyyar LP mai hamayya ce ta rika zuwa ta uku.
Mayakan Boko Haram sun kashe mutum biyu a a wata cibiyar tattara sakamakon zabe da ke Kuareta, kilo mita 20 nesa da garin Damaturu. Gwamnati ta tabbatar da harin.
Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta sanar da samun nasarar cafke wasu da ake zargin ƴan daba ne da ke shirin farmakar jami'an hukumar zaɓe a zaɓen da ake a jihar
Yayin da ake ci gaba da zaben cike gurbi a Plateau, masu kada kuri'a sun tsare wani jami'an hukumar INEC kan rashin kawo isassun kayayyakin zabe a Jos.
Kungiyar CAN reshen jihar Taraba ta karyata jita-jitar cewa ta tilasta dan takarar jam'iyyar SDP janyewa dan takarar PDP a zaben da ake gudanarwa na cike gurbi.
A ranar Asabar ne sojoji suka kama wasu mutane biyu ciki har da shugaban matasa a karamar hukumar Afikpo yayin zaben maye gurbin Sanatan Ebonyi ta Kudu.
Zaben Najeriya
Samu kari