Farfesa Mahmood Da Kwamishinoni INEC Suna Ganawar Sirri Kan Zaben Gwamnoni

Farfesa Mahmood Da Kwamishinoni INEC Suna Ganawar Sirri Kan Zaben Gwamnoni

  • Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban hukumar zabe mai zaman kanta INEC ya yi taron sirri da kwamishinonin hukumar
  • An yi wannan taron ne biyo bayan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa ta yi na bawa INEC damar sake saita na'urar BVAS
  • Daga karshe hukumar ta INEC ta dage yin zaben gwamnonin jihohi da yan majalisun jiha daga ranar 11 ga watan Maris zuwa ranar 18

FCT Abuja - Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, da kwamishinoninsa a halin yanzu suna taro.

Wannan taron ba zai rasa nasaba ba da zaben gwamnoni da yan majalisar jihohi da aka shirya yi a ranar 11 ga watan Maris na 2023.

Farfesa Yakubu
Shugaban INEC Da Kwamishinoni Suna Ganawar Sirri Kan Zaben Gwamnoni. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Wakilin The Punch ya gano cewa taron da aka fara tun misalin karfe 7 na yamma har yanzu ba a kammala ba a lokacin wallafa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: INEC Ta Ɗage Zaben Gwamnoni da Yan Majalisa a Hukumance, Ta Faɗi Sabuwar Rana

Sahara Reporters ta rahoto cewa an gano suna tattaunawa ne kan yiwuwar yin zaben gwamnoni da yan majalisun jihohi a wannan Asabar din ko kuma daga zaben da mako daya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A baya, an shirya yin zaben ne a ranar 11 ga watan Maris.

Wannan matakin sauya ranar zaben da INEC ta yi na zuwa ne a ranar Laraba bayan kotun sauraron karar zaben shugaban kasa a Abuja ta bawa hukumar ikon sake saita na'urar BVAS.

Kotun, a hukuncin da alkalai uku suka amince cewa da shi, ta ce hana INEC sake saita na'urar na BVAS zai shafi nagartar zaben gwamna da yan majalisar da za a yi a gaba.

Ta yi watsi da bukatar da jam'iyyar Labour da dan takarar ta Peter Obi suka shigar na hana hakan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: INEC Ta Samu Nasara, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Buƙatar Peter Obi

A cewar kotun, amincewa da bukatar Obi da jam'iyyar Labour zai zama "tauye wa INEC hakkin yin aikinta."

An kira taron gaggawa na shugabannin INEC bayan hukuncin kotu.

Hukumar INEC ta dage zaben gwamnoni da yan majalisun jihohi

A karshen taron, hukumar ta INEC ta sanar da dage yin zaben gwamnonin jihohi da na yan majalisun jiha a ranar Asabar 11 ga watann Maris.

A yanzu hukumar ta ce za a yi zaben gwamnonin ne a ranar Asabar 18 ga watan Maris na 2023, kamar yadda wata majiya ta sanar da Daily Trust.

Bayanai sun ce INEC ta nemi karin satin dayan ne domin samun daman sake saita na'urar BVAS kafin zaben gwamnonin da yan majalisun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel