Muna Jiran Hukuncin Kotun ƙoli Akan Lamarin Shekarau Inji NNPP

Muna Jiran Hukuncin Kotun ƙoli Akan Lamarin Shekarau Inji NNPP

  • Malam Ibrahim Shekarau dai ya yadda mangwaro ne ya huta da ƙudan NNPP da kujerar su.
  • An rufe yin rijistar yan takarkaru, NNPP ta shigar da ƙara sau biyu tana nasara kan INEC amma INEC ta dangana Kotun Koli.
  • Ana sa rai juma'a za'a zartar da hukuncin karshe wanda daga shi sai Allah ya isa kuma.

Tun bayan ayyana sunan Malam Ibrahim Shekarau a matsayin wanda ya lashe zaɓen majalisar dattijai ta Kano ta tsakiya ake ta samun maganganu masu karo da juna akan matakin da za'a ɗauka akan wannan kujera.

Duba da Malam Ibrahim Shekarau yace baya son kujerar, kuma ya fice daga jam'iyyar ta NNPP.

Bugu da ƙari, tuni aka bawa yan takarkari shaidar zaɓen su da akayi amma banda Shekarau ko Rufai Hanga.

Kara karanta wannan

"Ba Zamu Yarda NNPP ta Haddasa Mana Rikici a Zaɓe Mai Zuwa Ba" - Gwamnatin Kano

Shekarau
Muna Jiran Hukuncin Kotun ƙoli Akan Lamarin Shekarau Inji NNPP Hoto: UGC
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A wani salo na wanke zato, jam'iyyar NNPP ta bakin ciyaman ɗin ta, Farfesa Rufai Ahmed yace, jam'iyyar na nan tana dakon matakin da kotun ƙoli zata ɗauka akan wannan kujerar majalisar dattawan Kano ta tsakiya.

Ya nuna kwarin gwuiwar sa akan cewa, za'a bawa jam'iyyar hakkinta da aka kwace mata.

Alkali ya faɗawa Jaridar The Nation cewar, ana saran za'a fadi wannan hukunci ne a ranar juma'a ne zuwa.

Alƙali yace, Shekarau ya ajiye tafiyar NNPP da kujerar takarar sa lokacin da aka kulle fidda dan takara ne, kuma INEC taƙi ta amshi sunan wani sabon ɗan takarar da jam'iyyar ta bata domin fafatawa a zaɓen.

A cewar sa:

"INEC tace akwai matakai biyu kawai da za'ai haka. Mutuwa ko ajiye takara. Sai suka ce, tunda an kulle ɗaukar ɗan takara, mutuwa itace zaɓi kawai da muke da ita.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Rundunar Yan Sanda Ta Ayyana Neman Ɗan Takarar Gwamna da Wasu 9 Ruwa a Jallo

Yaci gaba da cewa:

"Muka je ƙaramar kotu, mukayi nasara, amma INEC taƙi yarda ta ɗaga ƙara zuwa kotun ɗaukaka ƙara, wanda nan ma mukayi nasara. Yanzu kuma sun sake zuwa kotun ƙoli. Yanzu ranar juma'a muke fatan sake samun nasara a hukuncin da kotun zata sake zartaswa". Inji shi.
"Ofishin mu na Kano ya shigar da ƙorafi gaban kotu na hana Shekarau amsar shaidar cin zaɓe.
Watakila shi yasa bai zo ba jiya.

Abubuwa 6 Da Tinubu Yake Buƙatar Tunkara Gadan-Gadan a Matsayin Shugaban Ƙasa.

NESG ce dai ta lissafa abubuwan da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ya kamata ya tunkara da zarar an rantsar dashi.

Ƙungiyar ta bada shawarar tattalin arziki tace, akwai buƙatar rage rashin aikin yi, bijiro da ababen more rayuwa da sauransu.

Rahoton nata zayyano ƙalubalen da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta da kuma tasirin su ga kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel