Peter Obi Ya Gargaɗi Magoya Bayansa Kan Yin Zanga-Zanga a Kotu

Peter Obi Ya Gargaɗi Magoya Bayansa Kan Yin Zanga-Zanga a Kotu

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya roƙi magoya bayan sa da kada suyi cincindo a harabar kotu domin yin zanga-zanga
  • Peter Obi yayi kira a gare su da kada su ce za su gudanar da zanga-zanga a kotuna lokacin da aka fara shari'ar zaɓe
  • Ɗan takarar ya sha alwashin ba zasu yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin sun kwato haƙƙin su a kotu wanda aka karɓe

Abuja- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya roƙi mabiyan sa da kada su gudanar da zanga-zanga a harabar kotu lokacin da aka fara shari'ar zaɓe. Rahoton Daily Trust

A yau ne dai kotun ɗaukaka ƙara zata saurari ƙarar da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta shigar tana neman da a dakatar da umurnin da aka ba Peter Obi, da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP,

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 Da Ya Wajaba Tinubu Tunkara Gadan-Gadan a Matsayin Shugaban Ƙasa

Atiku Abubakar, domin duba na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a wato (BVAS).

Peter
Peter Obi Ya Gargaɗi Magoya Bayansa Kan Yin Zanga-Zanga a Kotu Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Obi da Atiku sun samu umurnin ne daga kotu domin duba kayayyakin da INEC tayi amfani da su a zaɓen shugaban ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, hukumar INEC a nata ɓangaren tana son a dakatar da wannan umurnin saboda hakan zai kawo cikas ga zaɓen gwamnoni na ranar Asabar.

Peter Obi ya fito yayi magana a shafin sa na Twitter, inda ya buƙaci magoya bayan sa da kada su je suyi cincirindo a harabar kotu.

A kalmansa:

"A yayin da muka fita neman ƙwato haƙƙin mu daka ƙwace, ina roƙon OBIdients sa su mutunta harabar kotuna sannan su ba tawagar lauyoyin mu damar gudanar da ayyukan su cikin kwanciyar hankali da lumana."
"Harabar kotu ba wajen kamfe bane saboda haka kada a mayar da shi hakan. Ina roƙon Obidients da su cigaba da gudanar da harkokin kasuwancin su cikin zaman lafiya."

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Zata Soma Sauraren Koke-Koken INEC, Tinubu Atiku, da Obi

Zaɓen Gwamnoni: Jam'iyyar Labour Party Ta Musanta Haɗewa Da PDP a Jihar Kaduna

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar Labour Party ta musanta haɗewa da jam'iyyar PDP a jihar Kaduna.

Jam'iyyar ta ce ba ta ba haɗewa da wata jam'iyya a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel