Manyan Yan Siyasan Arewa 11 da Suka Taba Kasa A Zaben 2023

Manyan Yan Siyasan Arewa 11 da Suka Taba Kasa A Zaben 2023

Zaben 2023 ya zo abin mamaki da dama inda manyan jiga-jigan siyasa a Arewa da ba'ayi tsammanin zasu fadi suka sha kashi hannun wasu da ko saninsu ba'a yi ba.

Legit ta tattaro muku jerin wasu yan siyasa goma masu fada aji da suka taba kasa ba wuya a zabukan da ya gudana a 2023.

1. Atiku Abubakar

Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP ya sha bugu hannun Asiwaju Bola Tinubu na APC

2. Tanko Al Makura

Tanko Al Makura, tsohon gwamnan jihar Nasarawa kuma sanata mai ci ya sha kasa hannun Mohammed Onawa na PDP a zaben Sanata mai wakiltar Nasarawa ta kudu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

3. Ahmad Babba-Kaita

Sanata mai wakiltar mazabar Katsina ta Arewa ya sha wahala hannun Nasir Zangon-Daura.

Kaita ya koma PDP gabanin zaben fidda gwani duk da cewa shi ke wakiltar Buhari a majalisa.

4. Kabiru Gaya

Bayan shekaru 16 a majalisa, Kabiru Gaya ya fadi zaben komawa majalisa wakiltar Kano ta kudu hannun Kawu Sumaila na jam'iyyar Nigerian Peoples Party (NNPP).

5. Gabriel Suswam

Tsohon gwamna kuma Sanata ya fadi ba nauyi hannun Emmanuel Udende of the All Progressives Congress (APC) a zaben mai wakiltar Arewa maso gabashin Benue.

Arewa
Manyan Yan Siyasan Arewa 11 Suka Taba Kasa A Zaben 2023 Hoto: Ahmad Babba Kaita/Kabiru Gaya/Bala Ibn Na'Allah/Simon Lalong
Asali: Facebook

6. Abubakar Bagudu

Gwamnan Kebbi kuma shugaban kungiyar gwamnonin APC ya dauki darasi wajen tsohon ubangidansa da yaso ya yiwa ritaya, Adamu Aliero.

7. Bala Ibn Na’Allah

Shahrarren Sanata mai fada a ji a majalisar dattawa, Bala Ibn Na'Allah ya sha kasa hannun Garba Maidoki na jam'iyyar PDP a zaben wakiltar Kebbi ta kudu.

8. Darius Ishaku

Ga shi gwamna mai ci, gashi dan kudancin Taraba, amma duk da haka ya fadi ba nauyi hannun David Jimkuta na jam'iyyar APC.

9. Gudaji Kazaure

Duk da shahararsa matsayin abokin talaka da kuma yakin da yayi kwanakin baya da gwamnan CBN, Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kazaure/Roni/Gwiwa/Yankwashi a majalisar wakilai ba zai samu damar komawa ba.

Kazaure ya fita daga APC kuma yayi takara karkashin jam'iyyar ADC.

10. Samuel Ortom

Bayan baran-baran dinsa da Atiku da uwar jam'iyyar PDP, gwamna Samuel Ortom ya sha kasa hannun tsohon hadimnsa, Titus Zam na jam'iyyar APC.

Ortom ya yi niyyar wakiltar mazabar Arewa maso yammacin Benue.

11. Simon Lalong

Ga shi gwamna, ga shi shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, haka kuma gashi shugaban kwamitin kamfen Tinubu/Shettima, amma duk da haka ya fadi ba nauyi a zaben kujerar sanata.

Bayan jam'iyyar LP ta lashe zaben shugaban kasa a jiharsa ta Plateau, Lalong ya jijjigu hannun Napoleon Bali na jam'iyyar PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel