Magana ta Tabbata, INEC Ta Bada Uzurin Daga Zaben Jihohi Zuwa Mako Mai Zuwa

Magana ta Tabbata, INEC Ta Bada Uzurin Daga Zaben Jihohi Zuwa Mako Mai Zuwa

  • Hukumar INEC mai aikin shirya zabe a kasar nan tayi jawabi a kan dalilin daga zaben Jihohi
  • Barista Festus Okoye ya bada sanarwar cewa ana bukatar lokaci domin a iya saita na’urorin BVAS
  • Kwamishinan zaben ya ce karar da aka shigar a kotu bayan zaben shugaban kasa ya jawo hakan

Abuja - Hukumar INEC mai shirya zabe a Najeriya, ta tabbatar da batun daga zaben Gwamnoni da ‘yan majalisar dokokin jihohi zuwa wani makon.

Kafin yanzu, mun kawo rahoto cewa da alamar ba za a shirya zaben a karshen makon nan ba. Hukumar ta fitar da jawabi na musamman a shafinta.

Babban kwamishinan yada labarai da wayar da kan masu zabe na Hukumar INEC, Festus Okoye ya bada sanarwar daga zaben na tsawon mako guda.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Farfesa Mahmood Da Kwamishinoni INEC Suna Ganawar Sirri Kan Zaben Gwamnoni

Barista Festus Okoye ya shaidawa Duniya wannan a daren Alhamis, ya ce INEC ta na bukatar lokaci domin ta saita na’urorin BVAS da ake aiki da su.

Ana saita BVAS kafin zabe

Bayan an yi amfani da na’urorin wajen zaben shugaban kasa, Hukumar mai zaman kanta ta ce dole ne a sake yi masu saiti kafin a shiga zabe na Jihohi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Okoye ya bayyana cewa a ranar 3 ga watan Maris, kotun sauraron karar zaben shugaban kasa ta ba wasu jam’iyyu damar duba kayayyakin zabe.

INEC.
Shugabannin INEC Hoto: @INECNigeria
Asali: Twitter

"Daga cikin kayan da kotu ta amincewa jam’iyyun siyasa duba akwai na’urori 176, 000 na BVAS da suke ajiye a ofisoshin INEC a kananan hukumomi.
Ganin zaben Gwamnoni da majalisun dokoki ya tunkaro, kuma babu tsayayyen lokacin duba kayayyakin aiki, INEC ta nemi kotu ta janye umarninta.

Kara karanta wannan

Zaben gwamna: INEC ta fito da kayan aikin zabe, ta fara raba su a wata jihar Arewa

Dalili kuwa saboda a iya gudanar da zabe na kwarai. Misali, akwai takamaimen lokaci da ranar da za a iya amfani da na’urar BVAS wajen shirya zabe.
Tun da an yi amfani da su a zaben shugaban kasa da majalisar tarayya a ranar 25 ga watan Fubrairun 2023, dole a sake yi masu saiti kafin zaben jihohi."

- Festus Okoye

INEC ta ce lokaci ya kure mata

Daily Trust ta rahoto Kwamishinan hukumar ya ce kotu ta bada dama ayi wannan aiki, amma umarnin ya zo a makare ta yadda ba za a iya kammalawa ba.

A karshe Okoye ya ce saboda wannan ne za ayi zaben a ranar 18 ga watan Maris na 2023, yake cewa babu yadda suka iya, dole suka dauki wannan matakin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel