Mazabu 8 da Za a Sake Zaben Sanatoci a Najeriya a Ranar 11 Ga Maris

Mazabu 8 da Za a Sake Zaben Sanatoci a Najeriya a Ranar 11 Ga Maris

  • Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayyana mazabun da za a sake zaben sanataoci saboda tasgaron da aka samu
  • INEC ta fitar da jerin wadanda suka lashe zabe tare da ba su takardun shaida a hedkwatar hukumar a jiya Talata 7 ga watan Maris
  • Za a yi zaben gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a Najeriya a ranar Asabar 11 ga watan Maris mai zuwa kamar yadda aka tsara

FCT, Abuja - Bayan kammala zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya a Najeriya, hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fitar da sunayen wadanda suka yi nasara da kuma mazabun da suka fito.

Sai dai, duk da tabbatar da zabukan mazabu 109 a fadin kasar nan na sanatoci, hukumar ta ce akwai inda dole za a sake yin zaben saboda wasu dalilai.

Kara karanta wannan

IWD2023: Mata 2 da Suka Shiga Jerin ‘Yan siyasa 109 da Za su Zama Sanatocin Najeriya a 2023

A cewar INEC, za a sake zaben sanata a mazabu bakwai, kana an bar wata kujera babu kowa saboda mutuwar daya daga ‘yan takarar da suka neme ta.

INEC ta ce za a sake zaben sanatoci a wasu mazabu a Najeriya
Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) Mahmud Yakubu | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Idan baku manta ba, Legit.ng Hausa ta kawo muku cikakken jadawalin wadanda suka lashe zaben da ma jam’iyyunsu a fadin kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ruwaito cewa, jam’iyyar APC ta samu kujerun sanata 55, jam’iyyar PDP ta samu 33, sai kuma jam’iyyar Labour da ta samu kujeru 7.

A cewar shugaban hukumar zaben ta INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, jam’iyyun siyasa takwas ne suka yi takara a wannan zabe na bana na sanata.

Jam’iyyun kuwa sun hada da APC, PDP, Labour, SDP, APGA, NNPP, ADC da YPP, kamar yadda jadawalin ya bayyana.

Yaushe za a sake zabe a mazabun da lamarin ya shafa?

A cewar INEC, za a sake zabukan ne a ranar 11 ga watan Maris tare da na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi da aka tsara a kasar.

Kara karanta wannan

Rikici: Duk da ayyana shi ya ci zabe, INEC ta cire sunan dan majalisar Kano zababbun 'yan majalisa

Ga dai jerin mazabun da za a sake zaben na sanata a ranar 11 ga watan Maris:

1. Mazabar Filato ta Tsakiya

2. Mazabar Kebbi ta Arewa

3. Mazabar Sokoto ta Gabas

4. Mazabar Sokoto ta Arewa

5. Mazabar Sokoto ta Kudu

6. Mazabar Yobe ta Kudu

7. Mazabar Zamfara ta Tsakiya

8. Mazabar Enugu ta Gabas (dan takara 1 ya mutu)

Idan baku manta ba, jim kadan bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe, INEC ta ba Bola Tinubu shaidar lashe zaben shugaban kasa a Najeriya na 25 ga watan Faburairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel