Yan Daban Siyasa Sun Yi Mummunan Karo a Bauchi, An Kashe Mutum Daya, Wasu 15 Sun Jikkata

Yan Daban Siyasa Sun Yi Mummunan Karo a Bauchi, An Kashe Mutum Daya, Wasu 15 Sun Jikkata

  • An yi kazamin karo tsakanin yan daban APC da PDP a jihar Bauchi gabannin zaben gwamna
  • Rikici ya barke yayin da dan takarar gwamnan APC, Saddique Baba Abubakar ya je kamfen a garin Duguri a jihar Bauchi
  • Mutane 15 sun jikkata sakamakon harbe-harbe da aka yi tsakanin bangarorin biyu sannan wani ya rasa ransa

Bauchi - Gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da cewar an kashe mutum daya yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da wasu yan daban siyasa suka yi karo a Duguri, karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.

Duguri ya kasance mahaifar gwamnan jihar, Sanata Bala Mohammed wanda ke neman zarcewa a karo na biyu karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed yana jawabi
Yan Daban Siyasa Sun Yi Mummunan Karo a Bauchi, An Kashe Mutum Daya, Wasu 15 Sun Jikkata Hoto:Leadership
Asali: UGC

Darakta Janar na kungiyar kamfen din Bala Mohammed, Farouk Mustapha ya yi zargin cewa yan daban 'ya'yan jam'iyyar APC ne a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Hukumar INEC Ta Tabbatar Da Emmanuel Bwacha Matsayin Dan Takaran Gwamnan Taraba na APC

Mustapha ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati a safiyar Alhamis, jaridar Nigerian Tribune ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya yi ikirarin cewa rikicin ya fara ne lokacin da dan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Ambasada Saddique Baba Abubakar ya je Duguri don kamfen din karshe inda ya samu rakiyar manyan yan siyasa daga fadin kasar.

A cewar Mustapha:

"Yau na daya daga cikin rana mafi muni a tarihin siyasar jihar Bauchi, dukkanin yan takarar jam'iyyu daban-daban sun sanya hannu a yarjejeniyar zaman lafiya a hedkwatar yan sanda na jihar kamar yadda aka saba duk lokacin zabe.
"Sai dai kuma, dan takarar APC, Air Marshal Sadique Baba Abubakar mai ritaya bai hallara ba, mataimakinsa ne kawai ya halarta yana mai nuna rashin girmamawa ga zaman lafiya da amincin da ke a jihar Bauchi."

Kara karanta wannan

Muhimman Abubuwa 10 Game Da Nasiru Yusuf Gawuna Dan Takarar Gwamnan Kano Na APC

Ya ci gaba da cewa:

"Shugabannin APC da suka jagoranci yan ta'addan na yau sun yi ta'asa, sun razana mutane a garin Duguri, suna ta zage-zage da fasa allunan PDP da ke dauke da hotunan mai girma gwamna. Yan ta'addan sun kona motocin bas-bas, ofishoshin PDP da adaidaita sahu."

Rundunar yan sanda ta yi martani

Da take martani ga ci gaban, rundunar yan sandan jihar Bauchi ta bakin kakakinta, SP Ahmed Wakili ta bayyana cewa:

"A yau dan takarar gwamna na APC ya je yin gangami da misalin karfe 4500hrs, yayin da yake kauyen Duguri, karkashin gudunmar Yuli-Yin, karamar hukumar Alkaleri, rikci ya barke yayin gangamin inda aka raunata mutum 14. Daga cikin 14 da suka jikkata, an dauki shida zuwa cibiyar kiwon lafiya a Duguri, inda aka yi masu magani tare da sallamarsu."
“Daga cikin wadanda aka yi wa magani da sallama sune Suleiman Adamu, Danlami Musa, Kabiru Sani, Rabi, Abdulrasheed Bala da Tanko Wakilin Pawa, dukkansu mazauna kauyen Duguri."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Babbar Kotu Ta Tsige Ɗan Takara a Jihar Arewa Kwana 3 Gabanin Zabe

Ya kuma bayyana cewa mutum takwas sun ji mummunan rauni, inda aka tura su babban Asibiti, Alkaleri. Sai dai kuma ya ce bai da masaniya kan wadanda suka mutu.

Jam'iyyar APC ta yi tsokaci

A nasa martanin, kwamitin yakin neman zaben gwamnan APC ta bakin kakakinsa, Salisu A Barau, ya yi watsi da zargin PDP, rahoton Independent.

Barau ya ce wasu da ake zaton yan daban haya ne dauke da bindigogi sun bude wuta kan ayarin dan takarar gwamnan APC a Bauchi a garin Duguri, mahaifar Gwamna Bala Mohammed.

Ya bayyana cewa shaidu sun ce an ta jiyo karar harbi ba kakkautawa a wajen kamfen din, wanda hakan yasa jami'an tsaro da ke wajen gaggauta zuwa wajen harbin.

Sai dai ya ce a cikin haka ne harbi ya samu wasu ciki harda jami'an tsaro inda aka kwashe su zuwa asibiti.

DSS ta ce ta gano shirin ta da zaune tsaye bayan zaben gwamnoni

A wani labarin kuma, hukumar DSS ta gargadi yan Najeriya a kan kulle-kullen da wasu ke yi na son kawo rudu a kasar bayan zaben gwamnoni

Asali: Legit.ng

Online view pixel