Jam'iyyar ADP Ta Ƙaryata Jita-Jitar Da Ake Yaɗawa Kan Ɗan Takarar Gwamnanta Na Kaduna

Jam'iyyar ADP Ta Ƙaryata Jita-Jitar Da Ake Yaɗawa Kan Ɗan Takarar Gwamnanta Na Kaduna

  • Jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) ta karyata jita-jitar da ake yaɗawa akan ɗan takarar gwamnan ta na jihar Kaduna
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa ƙarya ce tsagwaron ta jita-jitar da ake yaɗawa cewa Sani Sha'aban ya janye daga takarar gwamna
  • A cewar jam'iyyar, Sani Sha'aban wanda suruki ne a wajen shugaba Buhari, ba zai taɓa janyewa daga takarar gwamnan ba

Jihar Kaduna- Jam'iyyar Action Democratic Party (ADP) tayi watsi da jita-jitrar dake yawo cewa ɗan takarar gwamnan ta a jihar Kaduna, Sani Sha'aban, ya janyewa wani ɗan takara.

Jam'iyyar ADP ta bayyana cewa Sani Sha’aban, wanda surukin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne, shine zaɓin al'ummar jihar domin zama gwamnan su

Sha'aban
Jam'iyyar ADP Ta Ƙaryata Jita-Jitar Da Ake Yaɗawa Kan Ɗan Takarar Gwamnanta Na Kaduna Hoto: Radio Nigeria Kaduna
Asali: UGC

A wata sanarwa da sakataren jam'iyyar na ƙasa, Victor Fingesi, ya fitar ranar Alhamis a Kaduna, ya buƙaci ƴaƴan jam'iyyar da al'ummar jihar da suyi watsi da jita-jitar da ake yaɗawa.

Kara karanta wannan

"Zan Tattauna Da Ƴan Bindiga Idan Aka Zaɓe Ni" Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Kaduna

Sanarwar ta kuma yi kira ga waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a da su fito ƙwan su da ƙwarƙwatar su, su kaɗawa ɗan takarar ƙuri'a a ranar zaɓe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwar na cewa:

"Jam'iyyar mu ta cikin takaici ta lura da labaran ƙanzon kurege da ake yaɗawa na cewa ɗan takarar gwamnan mu a jihar Kaduna yayi haɗaka da wani ɗan takarar wata jam'iyya domin janyewa ko mara masa baya."
“Wannan jita-jitar ko shakka babu an kitsa ta ne domin ta ɓata sunan jam'iyyar mu da ɗan takarar gwamnan ta a zaɓen ranar Asabar, 18 ga watan Maris, 2023."
"Ko tantama babu, ɗan takarar gwamnan jam'iyyar mu, Sani Sha'aban, wanda shine zaɓin al'ummar jihar Kaduna, har yanzu shine ɗan takarar dake kan gaba a zaɓen.
"Sannan akwai takaici ta yadda har yanzun a irin wannan zamanin, akwai wasu ƴan siyasar da za su iya kitsa irin wannan labaran kanzon kuregen domin ɓata masa suna ko kawo ruɗani a cikin al'umma.

Kara karanta wannan

Bayan Ya Garzaya Kotu, Peter Obi Ya Aikewa Magoya Bayansa Da Wani Muhimmin Gargaɗi

Jam'iyyar ta bayyana cewa Sha'aban ya shiga takarar gwamnan ne domin yayi nasara, saboda haka ba zai taɓa janyewa wani ɗan takara daban ba.

Dan Takararmu Na Gwamna a Jihar Katsina Bai Janye Ba, Inji PDP

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar PDP a jihar Katsina ta fito fili ta ƙaryata jita-jitar da ake yaɗawa kan ɗan takarar gwamnanta na jihar.

Jita-jita ta bazu cewa ɗan takarar gwamnan jam'iyyar na jihar, Yakubu Lado, ya janye daga takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel