Jihar Borno
Halin kunci a Najeriya ya fara sauya salo yayin da wasu matasa suka fito zanga-zanga a jihar Borno tare da yin barazanar shiga kungiyar Boko Haram.
Jirgin rundunar sojin NAF ya yi nasarar sheƙe kwamandoji uku na ƙungiyar ta'addancin ISWAP a wani ruwan bama-bamai da ya kai mafakarsu a jihar Borno.
Rahotanni sun kawo cewa dakarun tsaro sun kama wasu matan 'yan Boko Haram da yaransu a hanyarsu ta komawa wajen mazajensu a Tafkin Chadi daga jihar Borno.
Yayin da ake zargin shugaban sansanin Bama da ke jihar Borno, Abbah Tor da karkatar da wasu kayayyaki, Gwamna Zulum ya fatattake shi daga sansanin.
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya umurci a gudanar da azumin kwana daya a jihar don samun saukin tsadar rayuwa da rashin tsaro.
Kwamishinar harkokin mata da walwala, Hajiya Zuwaira Gambo, ta bayyana cewa mutuwar shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau, ta taimaka wajen samun zaman lafiya.
Gwamnatin jihar Borno ta bayyana cewa tubabban mayakan Boko Haram, sun yi tuba ta gaskiya kuma ba za su sake komawa kan mummunar dabi'ar yin kashe-kashe ba.
Jami’an ‘yan sanda sun kama wasu mutum biyu, mace da namiji turmi da tabarya a cikin cocin ADC kwalejin ‘yan sanda da ke Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Babagana Zulum ya rabawa marasa gata kayan abinci a yankin Bama ta jihar Borno. Hakan na daga cikin kokarinsa na tallafa wadanda rikicin Boko Haram ya ritsa da su.
Jihar Borno
Samu kari