Gwamnatin Borno Ya Bayyana Abinda Ya Karya Lagon Yan Ta'addan Boko Haram

Gwamnatin Borno Ya Bayyana Abinda Ya Karya Lagon Yan Ta'addan Boko Haram

  • Gwamnatin Borno ta bayyana abubuwan da suka jawo ƴan ta'adda suka zabi miƙa wuya tare da aje makamansu a jihar da ke Arewa maso Gabas
  • Kwamishinar harkokin mata da walwala, Hajiya Zuwaira Gambo, ta ce mutuwar Sheƙau, faɗan ISWAP da Boko Haram, da matakan Zulum sun taimaka sosai
  • Ta kuma maida martani ga matar da ta yi zargin cewa sojoji na riƙe da mazajensu da babu ruwansu a barikin Giwa a Maiduguri

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno karkashin Gwamna Babagana Umaru Zulum ta bayyana muhimmin abubuwan da suka karya lagon ƴan ta'adda a jihar.

Kwamishinar harkokin mata da walwala, Hajiya Zuwaira Gambo, ta ce mutuwar Abubakar Sheƙau, na ɗaya daga cikin abinda ya sa ƴan ta'addan suka ja da baya.

Kara karanta wannan

Bayin Allah da yawa sun mutu yayin da ƴan bindiga suka buɗe wa jama'a wuta a jihar Arewa

Gwamna Babagana Umaru Zulum.
Gwamnatin Borno Ya Bayyana Abinda Ya Karya Lagon Yan Ta'addan Boko Haram Hoto: Prof. Babagana Umaru Zulum
Asali: Twitter

Idan baku manta ba, Shekau, shugaban Boko Haram ya bindige kansa har lahira lokacin da mayaƙan ISWAP da suke takun saƙa suka farmaki sansaninsa a dajin Sambisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hajiya Zuwaira ta ce wannan mutuwa ta Sheƙau ta taimaka matuƙa gaya wajen miƙa wuyan da ƴan ta'addan suka riƙa yi rukuni bayan rukuni, Leadership ta ruwaito.

Kwamishinar ta ƙara da cewa faɗan da ya kaure tsakanin ISWAP da magoya bayan Sheƙau da kuma matakan da Gwamna Zulum ya ɗauka sun taimaka a lamarin.

A cewarta, waɗan nan dalililai da ta ambata da ƙarin wasu sun bada gudummuwa a zaman lafiyar da aka samu yanzu a sassan jihar Borno.

An saki ƴan ta'addan da suka miƙa wuya 500

Ta bayyana haka ne ranar Laraba, 14 ga watan Fabrairu, 2024 yayin da take mayar da martani ga ɗaya daga cikin waɗanda suka kubuta daga sharrin Boko Haram, Hajiya Gana.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya fadi dalili 1 da ya sa tubabbun mayakan Boko Haram ba za su koma kashe-kashe ba

Hajiya Gana ta yi zargin cewa an tsare wasu mazajensu da yaransu da ba su ji ba kuma ba su gani ba a barikin Giwa da ke Maiduguri, yayin mamayar sojoji.

Da take musanta zargin, kwamishinar matan ta ce gwamnati ta wanke tubabbu 500 daga zargin hannu a ayyukan ta'addanci kuma tuni aka sako su daga barikin sojoji.

Yan bindiga sun kai farmaki gidan sanata

A wani rahoton na daban Miyagun ƴan bindiga sun kai hari gidan sanatan Imo ta Arewa, Sanata Patrick Ndubueze ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu, 2024.

Rahotanni daga majiya mai ƙarfi sun nuna cewa Sanatan ya tsallake rijiya da baya a harin wanda aka yi nufin halaka shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel