Jam'iyyar PDP Ta Fusata, Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyyar da Sakatare, Ta Faɗi Laifin da Suka Tafka

Jam'iyyar PDP Ta Fusata, Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyyar da Sakatare, Ta Faɗi Laifin da Suka Tafka

  • Babbar jam'iyyar adawa PDP ta jihar Borno ta dakatar da shugaban jam'iyya na ƙaramar hukumar Jere, Muhammad Mustapha da sakatare
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa ta ɗauki wannan matakin ne kan shugabannin biyu saboda ba su ganin girman mambobin kwamitin gudanarwa na jiha
  • Amma dakataccen sakataren ya maida martanin cewa matakin ba zai yi tasiri ba saboda ya saɓa wa kundin dokar da aka kafa PDP

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Peoples Democratic Party (PDP) ta jihar Borno ta dakatar da shugaban jam'iyyar da sakatare na ƙaramar hukumar Jere da ke jihar.

Babbar jam'iyyar adawa ta bayyana cewa ta ɗauki wannan mataki kan kusoshin biyu saboda zarginsu da rashin mutunta shugabannin PDP na jiha.

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Arewa a gaban babbar kotu, bayanai sun fito

Jam'iyyar PDP ta ɗauki mataki a Borno.
Borno: PDP Ta Dakatar da Shugaban Jam'iyya da Sakatare Kan Muhimmin Abu 1 Hoto: OfficialPDP
Asali: Twitter

Shugaban PDP na jihar Borno, Zanna Gazama, shi ne ya tabbatar da haka ga manema labarai ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu, 2024, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa PDP ta dakatar da shugaba da sakatare?

Gazama ya ce an dakatar da shugaban PDP na ƙaramar hukumar Jere saboda ya daina halartar tarukan jam'iyya tun 2022 kuma ba wanda ya isa ya ba shi umarni daga matakin jiha.

"An dakatar da Muhammad Mustapha, shugaban PDP na Jere saboda ya daina zuwa taron jam'iyya tun 2022 kuma baya kallon kowa da gemu a kwamitin gudanarwa na jiha.
"Game da batun sakatare kuma, bayan mun dakatar da shugaban jam'iyya, ya kira taron shugabanni kuma ya yi ƙoƙarin haɗa kansu su yi fatali da matakin da PDP ta ɗauka.
"Sakamakon haka, jam'iyyar PDP ba ta da wani zaɓi da ya wuce shi ma ta dakatar da shi."

Kara karanta wannan

Mata sun fito kan tituna zanga-zanga, sun aike da muhimmin saƙo ga ministan Tinubu

- Zanna Gazama.

Wane mataki suka ɗauka?

Da yake maida martani yayin hira da ƴan jarida a sakateriyar NUJ da ke Maiduguri ranar Alhamis, dakataccen sakataren PDP na Jere, Usman Haruna ya yi watsi da matakin.

Haruna ya ce dakatarwan da aka masu ba ta da amfani domin ta saɓa wa tsarin kundin mulkin jam'iyyar PDP.

Deleget ta haihu a wurin zaɓe

A wani rahoton kun ji cewa zaben fidda gwanin jam'iyyar PDP a jihar Edo ya zo da abun murna da farin ciki yayin da wata Deleget mace ta haifi zankaɗeɗen jariri namiji.

An ce matar ta fara naƙuda ne a wani Otal da aka aje su, ita da sauran deleget, inda mutanen da ke wurin suka taimaka mata har ta haihu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262