'Yan Gudun Hijira Sun Fusata Gwamna Zulum Bayan Sun Yi Abu 1 Tak

'Yan Gudun Hijira Sun Fusata Gwamna Zulum Bayan Sun Yi Abu 1 Tak

  • Gwamnan jihar Borno ya nuna takaicinsa kan zanga-zanga wasu ƴan gudun hijiara suka yi a jihar kan yunwa
  • Gwmnan ya bayyana yin zanga-zangar a matsayin butulci duba da yadda yake bakin ƙoƙarinsa a kansu
  • Gwamna Zulum wanda ya yi bayani cikin fushi a gaban ƴan gudun hijirar da ke a Mafa ya ce ya yi iyakar abin da zai iya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya caccaki ƴan gudun hijirar da suka yi zanga-zanga a sansanin gudun hijira na Mafa da ke ƙaramar hukumar Mafa a jihar Borno.

Ƴan gudun hijirar a yayin zanga-zangar sun koka da yunwa, tare da yin barazanar shiga sahun ƴan ta’addan Boko Haram a cikin daji.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: NLC ta samu gagarumar matsala kan zanga-zanga, bayanai sun fito

'Yan gudun hijira sun fusata Gwamna Zulum
Gwamna Zulum ya fusata kan barazanar 'yan gudun hijira Hoto: @govborno
Asali: Twitter

Ƴan gudun hijira sun yi zanga-zanga a Borno

Ɗimbin ƴan gudun hijira kimanin 50,000 a mahaifar Zulum da ke Mafa, sun tattara kayansu don nuna rashin amincewarsu da ƙarancin abinci, inda suka yi barazanar ficewa daga sansanin saboda yunwa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lamarin na Mafa ya biyo bayan irin wannan zanga-zangar da ƴan gudun hijirar suka yi a sansanin ƴan gudun hijira na Dikwa kwanakin baya da suka wuce.

Jaridar Leadership ta ce da yake jawabi ga ƴan gudun hijira kimanin 50,000 a mahaifarsa ta Mafa ranar Lahadi,  Gwamna Zulum ya bayyana su a matsayin masu butulci, yana mai cewa:

“Na yi muku iyakacin ƙoƙarina. Ba zan iya yin fiye da hakan ba."

Ya ce gwamnatinsa ta kashe sama da Naira biliyan 40 a cikin shekara guda wajen gudanar da ayyukan jin ƙai na ƴan gudun hijirar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun halaka shugaban al'umma a wani sabon hari

Wane martani Zulum ya yi wa ƴan gudun hijirar?

Ya kuma ƙara da cewa an aika da kayan agaji zuwa sansanin a lokuta da dama don haka ya bayyana halin ƴan gudun hijirar a matsayin irin na masu butulci marasa godiyar Allah, rahoton Premium Times ya tabbatar.

A kalamansa:

"Yau ƴan gudun hijira a sansanin ƴan gudun hijira na mahaifata ta Mafa, suna yin zanga-zanga tare da barazanar barin sansanin. Zanga-zangar wasu ɓata gari ne ke haddasa ta.
"Ƙarancin abincin da ake fama da shi yanzu ya karaɗe ko ina a duniya sannan yaƙin Rasha da Ukraine ya haddasa shi, ba wai kawai iyakarsa a jihar Borno ba.

Ya tunatar da ƴan gudun hijirar cewa a cikin shekara huɗu zuwa biyar da suka gabata, ya zo Mafa fiye da sau 30 domin raba kayan abinci da sauran kayayyaki, inda ya ce ba zai iya yin abin da ya wuce hakan ba.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ɗaliban fitacciyar jami'ar Arewa bisa zargin kashe rayukan bayin Allah

Zulum Ya Ayyana Ranar Yin Azumi a Borno

A baya rahoto ya zo cewa gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ware rana guda domin gudanar da azumi a jihar.

Gwamnan ya ware ranar yin azumin ne domin samun sauƙi kan tsadar rayuwa da matsalar rashin tsaro da ake fama da ita jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel