Iyalan Ƴan Boko Haram da Suka Tuba a Borno Sun Yi Barazanar Komawa Daji Kan Wani Dalili 1 Tak

Iyalan Ƴan Boko Haram da Suka Tuba a Borno Sun Yi Barazanar Komawa Daji Kan Wani Dalili 1 Tak

  • Iyalan ƴan ta'addan Boko Haram da suka miƙa wuya ga gwamnatin jihar Borno sun yi barazanar komawa daji da rayuwa
  • Zagaz Ola Makama ya ce iyalan ƴan ta'addan sun yi barazanar ne saboda tsananin wahalar rayuwa da yunwa da ke addabar su
  • Makama ya wallafa bidiyon iyalan a ɗango-ɗango da suka hada da mata da kananan yara dauke da kayayyakin su suna tafiya a daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Borno - Iyalan ƴan Boko Haram sa suka tuba suka miƙa wuya ga gwamnatin jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya sun yi barazanar komawa daji.

Iyalan sun yi wannan barazanar ne suna masu kafa hujja da tsananin wahalar rayuwar da suke fuskanta a muhallan da suke zama yanzu.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Matasa a Borno sun yi barazanar shiga Boko Haram, bayanai sun fito

Tsananin wahalar rayuwar na neman tilasta iyalan 'yan Boko Haram komawa daji a Borno.
Tsananin wahalar rayuwar na neman tilasta iyalan 'yan Boko Haram komawa daji a Borno. Hoto: @GovBorno, @ZagazOlaMakama
Asali: Twitter

Zaga Ola Makama, mai fashin baki kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da kasashen Afrika ta Yamma ya baiyana hakan a shafinsa na X a ranar Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ga bidiyon iyalan na tafiya cikin daji

Zaga Ola Makama ya ce iyalan ƴan Boko Haram din da ke zaune a Dikwa, karamar hukumar jihar Borno ne suka yi wannan barazanar saboda yunwar da ke addabar su.

Yayin da ya wallafa bidiyon iyalan ƴan ta'addan suna tafiya a daji dauke da kayayyakin su, Makama ya roki gwamnati da ta kai masu ɗauki.

An jiyo muryar wanda ke ɗaukar bidiyon yana yi wa mutanen magana a cikin wani yare, inda daga bisani bidiyon ya nuna dandazon mata da kananan yara a wani babban fili.

Kalli bidiyon a kasa:

Asali: Legit.ng

Online view pixel