Yajin aikin ASUU
Jami'ar Bayero da ke Kano (BUK) ta sanar da dakatar da gudanar da jarabawar zangon karatun farko na shekarar 2022/2023 saboda yajin aikin ƙungiyoyin ƙwadago.
NLC ta bayar da umurnin tsunduma yajin aikin ne a taron majalisar zartarwa na kungiyoyin kwadago na kasa da aka gudanar a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2023 a Abuja.
Harkoki sun daina tafiya a ma'aikatun tarayya da na jiha a babban birnin jihar Delta yayin da NLC ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Talata.
Yajin aikin NLC bai karɓu ɗari bisa ɗari ba a jihar Kaduna ranar Talata, bankuna da gidajen mai sun gudanar da ayyukansu kamar kullum ranar Talata.
Ƙungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta CONUA ta ƙi shiga yajin aikin gama-gari d aƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) da TUC suka fara a faɗin ƙasar nan.
Yayin da ake ci gaba da yajin aikin kungiyar NLC, kungiyoyi da dama sun tsunduma yajin aiki a Najeriya a kokarin bin umarnin kungiyar kwadago ta NLC.
Ma'aikatu, bankuna da sauran wuraren aiki sun ki tafiya yajin aiki, inda aka ga mutane na ayyukansu na yau da kullum a jihar Taraba, kenan, sun bijirewa umurnin NLC.
Kungiyar kwadago ta ƙasa NLC ta bi manyan sakatarriyar gwamnatin tarayya da na jiha a Filato sun sa kwaɗo da makulle, ma'aikata sun juya zuwa gidajensu.
Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin tarayya ta dauki gagarumin mataki don dakatar da yajin aikin sai baba ta gani da kungiyar kwadago suka shiga a ranar Litinin.
Yajin aikin ASUU
Samu kari