Yajin Aiki: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki a Rigimar NLC da FG

Yajin Aiki: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki a Rigimar NLC da FG

  • Majalisar dattawan Najeriya ta tsoma baki kan batun yajin aikin da ƙungiyoyin kwadago suka shiga a faɗin ƙasar nan
  • Yayin zaman ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, 2023, majalisar ta amince da kudirin da shugaban masu rinjaye ya gabatar kan yajin aikin
  • Ta kuma yi kira ga kungiyoyin NLC, TUC da kuma ASUU su janye wannan yaji domin nuna suna kishin ƙasa da bin doka sau da ƙafa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar dattawan Najeriya ta shiga tsakani da nufin kawo ƙarshen yajin aikin da ma'aikatan Najeriya suka fara tun ranar 14 ga watan Nuwamba, Channels tv ta rahoto.

Majalisar dattawa ta tsoma baki a yajin aikin ƴan kwadago.
Yajin Aiki: Majalisar Dattawa Ta Tsoma Baki a Rigimar NLC da FG Hoto: thenation
Asali: UGC

A ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, Majalisar dattawan ta yi kira ga manyan ƙungiyoyin ƴan kwadago, NLC, TUC da malaman jami'a (ASUU) su hakura su janye yajin aiki.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya bayyana yadda bankuna su ke aiki a lokacin yajin aiki

Sanatocin sun cimma matsaya ɗaya

Majalisar ta kuma ɗora wa shugabanninta karkashin Sanata Godswill Akpabio, alhakin zama da shugabannin ƙungiyoyin cikin gaggawa domin sasantawa kan buƙatunsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta cimma wannan matsaya ne biyo bayan kudirin da shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele, ya gabatar a zaman yau Laraba, The Nation ta ruwaito.

Sanatan ya yi wa kudirin take da, "Buƙatar ƴan kwadago su sakr tunani kan yajin aikin da su ke yi domin nuna kishin ƙasa da kuma bin doka da oda."

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan ma'aikata sun fara yajin aiki a faɗin Najeriya sakamakon cin mutuncin da aka yi wa shugaban NLC a jihar Imo ranar 1 ga watan Nuwamba.

Sun gindaya gwamnatin tarayya sharuɗɗan da zasu sanya su janye yajin aiki, ci har da bukatar kama duk masu hannu a lakaɗa wa shugabam NLC dukan tsiya.

Kara karanta wannan

Yajin aiki: Ribadu ya kira taron gaggawa da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC, Bayanai Sun Fito

Kotun Ɗaukaka Kara Ta Tanadi Hukunci Kan Zaɓen Nasarawa

A wani rahoton na daban kuma Kotun ɗaukaka kara ta shirya, ta tanadi hukunci domin raba gardama kan sahihin wanda ya lashe zaɓen Gwamnan Nasarawa.

A baya Kotun zaɓe ta tsige Gwamna Abdullahi Sule na APC, ta ayyana ɗan takarar PDP a matsayin zababben Gwamna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel