Yajin Aikin NLC: CONUA Kishiyar ASUU Ta Ƙi Shiga Yajin Aiki, Ta Bayyana Dalilanta

Yajin Aikin NLC: CONUA Kishiyar ASUU Ta Ƙi Shiga Yajin Aiki, Ta Bayyana Dalilanta

  • A cigaba da yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadagon Najeriya na NLC da TUC suke yi a fadin ƙasar nan, wata ƙungiya ta daban ta zaɓi ƙin shiga
  • Ƙungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta CONUA, wacce kishiyar ƙungiyar ASUU ce, ta yanke shawarar ƙauracewa shiga yajin aikin
  • Shugaban CONUA, Niyi Sunmonu, ya bayyana cewa NLC ba ta sanar da su kan shirin fara yajin aikin ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ƙungiyar malaman jami'o'in Najeriya ta CONUA ta yi ƙarin haske kan cewa mambobinta ba su shiga yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa NLC da TUC suka fara yi a faɗin ƙasar nan ba.

Ƙungiyar, a ƙarkashin jagorancin shugabanta na ƙasa Niyi Sunmonu, ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, cewa NLC da TUC ba su tuntube su ba kafin a fara yajin aikin, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Yajin NLC: Harkoki sun tsaya cak yayin da ma'aikata suka zaɓa wa kansu mafita a babban birnin jihar PDP

CONUA ta ƙi shiga yajin aikin NLC
NLC ta tsunduma yajin aiki inda ta kulle makarantu da bankuna Hoto: NLC HQ
Asali: Facebook

Meyasa CONUA ta ƙi shiga yajin aikin?

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, sanarwar ta ce:

"Ya zuwa lokacin da muke fitar da wannan sanarwar, TUC wacce CONUA ta gabatar da buƙatar yin haɗaka da ita ba ta sanar da matakin yajin aikin ba."
"Don haka ya kamata ƴan uwa masu girma su lura cewa CONUA ba za ta iya zama wani ɓangare na yajin aikin da ba a sanar da ita ba."
"Bugu da ƙari, har yanzu ba a kammala kafa tsarin alaƙa da TUC a hukumance ba."

Duk da umarnin da ƙungiyoyin ƙwadago suka bayar na tsunduma yajin aikin gama-gari daga tsakar daren ranar 14 ga watan Nuwamba, 2023, malaman jami'o'in sun cigaba da tsayawa kan matsayarsu ta ƙin shiga yajin aikin.

Al'amura Sun Tsaya Cak Kan Yajin Aiki a Delta

A wani labarin kuma, ma'aikata a jihar Delta sun ƙauracewa wuraren aikinsu saboda yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa NLC da TUC suka fara a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamban 2023.

Mambobin ƙungiyar kwadago da suka fito aikin tabbatar da yajin aikin sun garƙame kofar shiga Sakateriyar tarayya da ta jiha da ke kan titin Okpanam.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel