Yajin Aiki: Gwamnati Ta Shiga Ganawa da Kungiyoyin Kwadago a Ofishin Ribadu

Yajin Aiki: Gwamnati Ta Shiga Ganawa da Kungiyoyin Kwadago a Ofishin Ribadu

  • Gwamnatin tarayya ta shiga ganawa da shuwagabannin kungiyoyin kwadago don kawo karshen yajin aikin da kungiyoyin ke yi a fadin Najeriya
  • Ministan Kwadago Simon Bako Lalong da karamin minista Hon Nkeiruka Onyeajeocha da NSA Nuhu Ribadu suka halarci taron madadin gwamnati
  • A ranar Talata ne kungiyoyin kwadago bisa sanarwar shugaban TUC na kasa, Comrade Festus Osifo, suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnatin tarayya ta shiga ganawa da kungiyoyin kwadago da suka hada da NLC da TUC don tattauna hanyoyin da za a bi don kawo karshen yajin yajin gama gari da kungiyoyin suka shiga.

A cewar wani rahoto na NTA, taron yana gudana ne a ofishin Nuhu Ribadu, mai ba wa shugaban kasa Tinubu shawara kan harkokin tsaro.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC sun janye yakin aiki, sun bada dalili

Gwamnati da NLC
Ana sa ran tattaunawar, za ta kawo karshen yajin aikin da kungiyoyin kwadagon suka shiga a fadin Najeriya Hoto: Joe Ajaero
Asali: Twitter

Ministan Kwadago Simon Bako Lalong da karamin minista Hon Nkeiruka Onyeajeocha da NSA Nuhu Ribadu sun samu halartar taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyoyin kwadagon sun samu wakilcin shugaban kungiyar TUC, Comrade Festus Osifo, sakataren kungiyar NLC, Emmanuel Ugboaja, da sauran shugabannin kungiyar kwadagon.

NLC, TUC sun janye yajin aiki, sun fadi dalili

Legit Hausa ta ruwaito maku yadda kungiyoyin kwadago na kasa suka sanar da janye wa daga yajin aikin da suka shiga a fadin kasar.

Yajin aikin ya fara a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, domin zanga-zanga a kan dukan da aka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero.

Dalilin janye yajin aikin yan kwadago

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, an janye yajin aikin ne a daren ranar Laraba, 15 ga watan Nuwamba, bayan tattaunawa da shugabannin kungiyoyin suka yi da mai ba kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu.

Kara karanta wannan

Kungiyoyin kwadago sun yi gum kan batun janye yajin aiki, sun yi karin haske kan ganawarsu da FG

Ribadu ya bayyana cewa an kama mutum biyu da ke da hannu a harin da aka kai wa Ajaero.

Sai dai kuma, jaridar Vanguard ta rahoto cewa za a ci gaba da tattaunawa kan bukatun yan kwadagon.

Babban sakataren hadaddiyar kungiyar AUPCTRE, Kwamrad Sikiru Waheed, ya tabbatar da ci gaban ga manema labarai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel