Jerin Kungiyoyin Kwadago 19 Da Suka Bi Umurnin NLC Na Tsunduma Yajin Aiki a Najeriya

Jerin Kungiyoyin Kwadago 19 Da Suka Bi Umurnin NLC Na Tsunduma Yajin Aiki a Najeriya

  • Akalla kungiyoyi goma sha tara ne rahotanni suka bayyana cewa sun tsunduma yajin aikin da kungiyoyin kwadago na kasa suka tsunduma a fadin Najeriya
  • A daren ranar Litinin, kungiyoyin kwadagon suka sanar da fara yajin aikin sai baba ta gani a fadin kasar, wanda ya fara aiki a safiyar ranar Talata
  • Wannan yajin aikin, ana yin shi ne biyo bayan gazawar gwamnati na biayn bukatun kungiyoyin kwadagon, da kuma cin zarafin shugaban NLC da aka yi a Imo

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kawo yanzu, kungiyoyi 19 ne suka umurci ma’aikatansu da su bi umurnin kungiyoyin kwadagon kasar guda biyu na su shiga yajin aikin sai baba ta gani a fadin Najeriya.

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC ya gamu da babban cikas a jihar Ƙaduna yayin da ma'aikata suka rabu gida biyu

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa samar da matsaya kan tsunduma yajin aikin ne a taron majalisar zartarwa na kungiyoyin kwadago na kasa da aka gudanar a ranar 13 ga watan Nuwamba, 2023 a Abuja.

Joe Ajaero
A safiyar ranar Talata aka tashi da yajin aikin, wanda ya sa komai ya tsaya a Najeriya Hoto: Joe Ajaero
Asali: Twitter

Dalilin shiga yajin aiki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan matakin dai ya samo asali ne daga gazawar gwamnatin tarayya wajen magance matsalolin da suka addabi ma’aikata, kamar mafi karancin albashi, rashin tsaro, cin hanci da rashawa, da rashin shugabanci na gari.

Har ila yau, kungiyoyin sun gabatar da wasu bukatu, wadanda ake zargin gwamnati ta gaza cikawa biyo bayan rikicin da aka yi a jihar Imo.

Rikicin ne ya yi sanadin cin zarafin shugaban NLC, Mista Joe Ajaero, da wasu mambobin kungiyar kwadagon.

Ga jerin sunayen kungiyoyin:

  • Kungiyar malaman jami'o'i (ASUU).
  • Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU).
  • Kungiyar malaman makarantun kwaleji (CEASU).
  • Kungiyar malaman makarantun Polytechnics (ASUP).
  • Kungiyar ma'aikatan abin sha da taba ta kasa (NUFBTE).
  • Kungiyar manyan ma'aikatan makarantun Polytechnics ta Najeriya (SSANP).
  • Kungiyar likitoci da ma’aikatan fannin lafiya ta Najeriya (MHWUN).
  • Kungiyar malaman sashen fasahar kirkire-kirkire ta kasa (NAAT)..
  • Kungiyar ma'aikatan wasika da sadarwa ta kasa (NUPTE).
  • Kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya (NULGE).
  • Kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya (JSUN).
  • Kungiyar masu tattara rahoton aikin gwamnati, sarrafa bayanai da ma’aikatun hadin gwiwa na Najeriya (NUPSRSDPAW).
  • Kungiyar ma'aikatan tufafi ta kasa da kuma masu dinki ta Najeriya (NUTGTWN).
  • Kungiyoyin ma’aikatan jinya da na ungozoma na kasa (NANNM).
  • Kungiyar ma'aikatan bankuna, Inshora da cibiyoyin hada-hadar kudi ta Najeriya (NUBIFIE).
  • Kungiyar ma’aikatan jiragen ruwa ta Najeriya (MWUN).
  • Kungiyar ma'aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE).
  • Kungiyar ma'aikatan majalisa ta Najeriya (PSAN).
  • Kungiyar ma'aikatan jirgin kasa ta Najeriya (NURW).

Kara karanta wannan

NLC: yayin da ake ci gaba da yajin aiki, an bayyana yawan ma'aikatun da ke ciki tsundum

NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki

Kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito, kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC, sun umurci mambobinsu da su fara yajin aiki a fadin kasar, sakamakon harin da aka kaiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.

Kungiyoyin kwadagon sun umurci dukkanin kungiyoyin ma'aikata da ke karkashinsu, da su tsunduma yajin aikin, bisa umurnin majalisar zartaswa ta kungiyoyin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel