Yajin Aiki: Jami'ar Bayero da Ke Kano Ta Sanya Dalibai Cikin Mawuyacin Hali

Yajin Aiki: Jami'ar Bayero da Ke Kano Ta Sanya Dalibai Cikin Mawuyacin Hali

  • Yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka fara yi a faɗin ƙasar nan ya kawo cikas a ɓangarori da dama
  • Yajin aikin ya sanya jami'ar Bayero da ke Kano (BUK) dakatar da jarrabawar zangon karatun farko da ta ke tsaka da gudanarwa
  • Hukumar ta sanar da cewa za a cigaba da gudanar da jarrawabar ne idan aka kawo ƙarshen yajin aikin na ƙungiyoyin ƙwadago

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta sanar da dakatar da jarrabawar zangon farko da sauran ayyukan karatu na shekarar 2022/2023.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun muƙaddashin magatakardar jami’ar, Amina Abdullahi Umar, cewar rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Saudiyya ta bayyana dalilin da ya sanya ta hana fasinjoji 177 ƴan Najeriya shiga ƙasar

BUK ta dakatar da jarrabawa saboda yajin aiki
Yajin aiki ya sanya BUK dakatar da jarrabawa Hoto: buk.edu.ng
Asali: UGC

Dakatarwar a cewar sanarwar ya biyo bayan yajin aikin da ƙungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka shiga a faɗin ƙasar nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar kula da jami’ar ta umurci dukkan daliban da su kwantar da hankalinsu tare da jiran ƙarin umarni, rahoton Leadership ya tabbatar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, ya kamata a lura cewa jarabawar da ake yi ta kusa kai rabi, kuma da zarar an kammala yajin aikin za a cigaba da gudanar da jarrabawar.

A ranar Litinin ne ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya (ASUU) ta umurci mambobinta da su shiga yajin aikin.

Yajin aikin na zuwa ne a matsayin martani kan dukan da ƴan sandan Najeriya da gwamnatin jihar Imo suka yi wa shugaban NLC, Joe Ajaero.

Ɗalibai sun koka

Legit Hausa ta samu jin ta bakin wani ɗalibi mai karatu a jami'ar, Abubakar Yuguda, wanda ya nuna rashin jin daɗinsa kan dakatar da jarrabawar da aka yi saboda yajin aiki.

Kara karanta wannan

Yanzu: Majalisar dattawa ta tsoma baki kan yajin aikin ƙungiyoyin kwadago, ta ɗauki matsaya 1 tak

Ya yi nuni da cewa dakatar da jarrabawar koma baya ne ga ɗalibai waɗanda suke da abubuwa da dama da suke son yi bayan an kammala jarrabawar.

"Ba mu ji daɗin wannan dakatar da jarrrabawar ba domin yanzu baya za a mayar da mu saboda wannan yajin aikin." A cewarsa.

An mayar da ɗalibai gida a Legas

Yajin aikin da ƙungiyoyin ƙwadago na NLC da TUC suka tsunduma a faɗin ƙasar nan, ya sanya an mayar da ɗalibai gidajensu bayan sun je makarantu a Legas.

Ɗaliban na makarantun firamare da sakandare na gwamnati sun koma gida ne saboda yajin aikin da malaman makarantunsu suka shiga.

Ma'aikata a Taraba Sun Bijirewa NLC

A wani labarin kuma, ma'aikata a jihar Taraba sun ƙi bin umarnin ƙungiyar ƙungiyar ƙwadago na shiga yajin aikin da ta fara a faɗin ƙasar nan.

Ma'aikatan dai sun je wuraren ayyukansu ba kuma an buɗe bankuna da wuraren kasuwanci domin cigaba da hada-hada da al'amuran yau da kullum.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel