Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Gagarumin Mataki Yayin da Aka Fara Yajin Aikin Gama Gari

Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Gagarumin Mataki Yayin da Aka Fara Yajin Aikin Gama Gari

  • Gwamnatin tarayya ta kira taron tattaunawa da kungiyar kwadago don dakatar da yajin aikin gama gari da ke gudana
  • Ministan kwadago da daukar ma'aikata, Simon Lalong, ya dauki matakin a daren ranar Litinin bayan kungiyar kwadago ta kaddamar da yajin aikin gama gari
  • An tattaro cewa taron zai gudana ne tsakanin gwamnatin tarayya da shugabannin NLC da TUC a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba

FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta dauki gagarumin mataki bayan kungiyar kwadago ta kaddamar da yajin aikin gama gari a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, ministan kwadago da daukar ma'aikata, Simon Lalong, ya kira wani taro tare da shugabannin kungiyoyin TUC da NLC a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Yajin Aiki: Shugaba Tinubu Ya Fusata, Ya Ce Matakin ‘Yan kwadago Ya Sabawa Doka

Gwamnatin tarayya za ta tattauna da kungiyar kwadago
Gwamnatin Tarayya Ta Dauki Gagarumin Mataki Yayin da Aka Fara Yajin Aikin Gama Gari Hoto: Simon Lalong/@NLCHeadquarters
Asali: UGC

Majiyar da ta bayyana wannan, ta bayyana a takaice:

"Ministan ya kira wani taron tattaunawa da kungiyoyin kwadago a ranar Talata."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya magantu kan yajin aikin NLC

A gefe guda, Legit Hausa ta rahoto a baya cewa fadar shugaban kasa ta yi tir da kungiyoyin NLC da TUC da su ka dage sai sun tafi yajin-aiki bayan abin da ya faru da Joe Ajaero.

Mai taimakawa shugaban kasa a yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya ce ‘yan kwadago sun wuce gona da iri a damar da su ke da ita.

A Twitter Onanuga ya maida martani ya na cewa babu dalilin tafiya yajin-aiki a kasar. Ya na ganin gadara kurum ta jawo kungiyoyin ma’aikatan ke neman yaudarar gwamnati da kuma takurawa al’umma.

Legit Hausa ta lura cewa an dauki lamarin yajin aiki da karfi a garin Minna da ke jihar Neja.

Kara karanta wannan

NLC Ta Rubutawa Ma’aikatan Wuta, Makarantu Takardar Dunguma Yajin Aiki a Najeriya

Makarantu da dama ciki harda na kudi sun kora yara gida saboda yajin aikin yan kwadagon.

Wata uwa ta koka kan yadda kona mai don kai yaranta makaranta amma haka ta juyo da su saboda babu makaranta.

Ta ce:

“Wai ka kai yaronka ma makarantar kudi amma baka tsira ba. Babban abun ma ba’a sanar mana da wuri cewa babu makaranta ba sai da na kwashi yara daga Dutsen kura zuwa Tunga sannan ake cewa mu juya da su babu makaranta. Kuma mai mutum ya zuba a mota ba ruwa ba. Gaskiya ya kamata gwamnati ta dauki matakin gaggawa don ganin an magance wannan yajin aiki.”

ASUU tayi martanin shiga yajin aiki

A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta umarci ‘ya ‘yanta su ka shiga yajin-aikin da kungiyoyin NLC da TUC su ka kira a yau.

Shugaban ASUU na kasa, Emmanuel Osodeke ya aika da wasika zuwa ga duka rassan kungiyar, Premium Times ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Kungiyoyin Kwadago sun shiga yajin aiki sai baba ta gani kan lakadawa shugaban NLC duka

Farfesa Emmanuel Osodeke ya rubuta takarda zuwa ga shugabannin ASUU na yankuna da jihohi cewa su shiga yajin-aikin da aka tafi.

Shugaban kungiyar malaman jami’an kasar yake cewa ya kamata su bi sahun kungiyar ‘yan kwadago domin suna cikin ‘ya ‘yanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel