Yajin Aikin Gama Gari: Ma’aikatan Taraba Sun Bijire Wa Umurnin NLC, Kowa Ya Tafi Wajen Aiki

Yajin Aikin Gama Gari: Ma’aikatan Taraba Sun Bijire Wa Umurnin NLC, Kowa Ya Tafi Wajen Aiki

  • Yayin da kungiyoyin kwadago suka tsunduma yajin aikin gama gari a fadin Najeriya, ma'aikata a jihar Taraba sun bijirewa umurnin kungiyoyin
  • Ma'aikatu, bankuna da sauran wuraren aiki sun kasance a bude, inda aka ga mutane na ayyukansu na yau da kullum
  • Sai dai ana hasashen cewa bijirewa yajin aikin da ma’aikatan ke yi na iya zama dabarun da za su bi domin kaucewa kara jiran albashin da suke yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Taraba - An ga ma’aikatan jihar Taraba a wuraren ayyukansu daban-daban a ranar Talata, 14 ga watan Nuwamba, inda suka bijirewa umarnin kungiyar kwadago ta kasa, NLC, na shiga yajin aikin gama gari.

Kara karanta wannan

Yajin aiiki: Abu ya girmama, Ma'aikata sun sha mamaki yayin da suka fita wurin aiki a jihar Arewa

Wakilin jaridar The Nation ya ziyarci sakatariyar jihar inda akasarin ofisoshin ma'aikatun jihar suke, kuma ma'aikata sun dukufa da ayyukansu yayin da wasu ke shawagi a harabar sakatariyar.

Joe Ajaero
Duk da umurnin da kungiyoyin kwadago na kasar suka bayar, ma'aikatan jihar Taraba sun bijirewa yajin aikin Hoto: Joe Ajaero
Asali: Twitter

Haka zalika, al'amura na yau da kullun suna gudana a cikin bankunan jihar, yayin bude kasuwanci da safiyar Talata, kamar yadda rahoton jaridar ya bayyana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kokarin jin ta bakin shugaban NLC na jihar domin jin ta bakinsa a kan lamarin ya ci tura, saboda kin amsa kiran da aka yi masa.

Ba a biya ma'aikatan jihar albashin watan Oktoba ba

Sai dai wanin ma’aikaci ya bayyana cewa kungiyar NLC na zagaya wa cikin sakatariyar don tursasa ma'aikata bin umurnin kungiyar kwadagon.

Har yanzu ma’aikatan jihar basu samu albashin watan Oktoba ba wanda gwamnan ya bada umarnin a biya su da sabon mafi karancin albashi na N30,000.

Kara karanta wannan

NLC Ta Rubutawa Ma’aikatan Wuta, Makarantu Takardar Dunguma Yajin Aiki a Najeriya

Don haka ana hasashen cewa bijirewa yajin aikin da ma’aikatan ke yi na iya zama dabarun da za su bi domin kaucewa kara jiran albashin da suke yi.

NLC da TUC sun tsunduma yajin aiki

Mun ruwaito maku yadda kungiyoyin kwadago na Najeriya NLC da TUC, suka umurci mambobinsu da su fara yajin aiki a fadin kasar, sakamakon harin da aka kaiwa shugaban NLC, Joe Ajaero.

Kungiyoyin kwadagon sun umurci dukkanin kungiyoyin ma'aikata da ke karkashinsu, da su tsunduma yajin aikin, bisa umurnin majalisar zartaswa ta kungiyoyin, kamar yadda rahoton Legit Hausa ya nuna.

Shugaban TUC, Festus Osifo, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba, ya ce yajin aikin zai ci gaba da kasancewa har sai “gwamnati a dukkan matakai sun farga da alhakin da ya rataya a wuyansu.”

Me ya jawo shiga yajin aiki?

Legit ta ruwaito maku yadda shugaban kungiyar kwadago (NLC), Comrade Joe Ajaero, ya labarta yadda ya ci dukan tsiya a hannun jami'an tsaron da suka yi awon gaba da shi a ranar Laraba.

Ajaero ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ya karade kafofin watsa labarai a ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel