Ma'aikata a Jihar Delta Sun Kauracewa Wurin Aiki Kan Yajin Aikin NLC

Ma'aikata a Jihar Delta Sun Kauracewa Wurin Aiki Kan Yajin Aikin NLC

  • Ayyuka sun tsaya cak a Sakateriyar tarayya da ta jiha da ke Asaba, babban birnin jihar Delta biyo bayan umarnin NLC na shiga yajin aiki
  • Ma'aikatan jihar ba su fita wuraren ayyukansu ba, kuma an ga mambobin NLC sun je sun garƙame ma'aikatun tun ƙarfe 8:00 na safiya
  • Rahotanni sun bayyana cewa bankuna sun rufe ƙofofinsu duk da an ga suna sauraron kwastomomi

Ahmad Yusuf, gogaggen Edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Delta - Ma'aikatan jihar Delta sun yi zamansu a gida sakamakon matakin fara yajin aiki da manyan ƙungiyoyin kwadago na ƙasa NLC da TUC suka ɗauka.

Harkoki sun tsaya a Asaba babban birnin jihar Delta.
Ma'aikata a Jihar Delta Sun Kauracewa Wurin Aiki Kan Yajin Aikin NLC Hoto: thenationonline
Asali: UGC

Tun ƙarfe 8:00 na safiyar yau Talata, mambobin ƙungiyar kwadago da suka fito aikin tabbatar da yajin aikin sun garƙame kofar shiga Sakateriyar tarayya da ta jiha da ke kan titin Okpanam.

Kara karanta wannan

Yajin aikin NLC ya gamu da babban cikas a jihar Ƙaduna yayin da ma'aikata suka rabu gida biyu

Jaridar The Nation ta tattaro cewa mambobin NLC sun rufe wuraren aikin da ke Asaba, babban birnin jihar Delta, sun sa kwaɗo domin hana ma'aikata shiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An rufe makarantu a Asaba

Haka nan kuma harkokin karatu sun tsaya cak a makarantun sakandire da ke cikin ƙwaryar birnin Asaba yayin da ɗalibai suka koma gida saboda babu malamai.

Duk da bankuna suna sauraron kwastomominsu amma ƙofofin shiga harabar bankunan a kulle su ke a yau Talata, 14 ga watan Nuwamba, 2023.

Har ila yau, an samu cikas a gudanar da ayyuka a gidan gwamnatin jihar Delta, yayin da ma’aikata suka gaza zuwa wajen aikinsu.

Idan baku manta ba, kungiyoyin kwadago na kasa sun umarci ƙawayensu da rassan jihohi su fara yajin aiki daga ranar 14 ga watan Nuwamba, 2023.

Sun ɗauki wannan matakin ne saboda lakaɗa wa shugaban NLC na ƙasa dukan tsiya da aka yi a jihar Imo a makon da ya gabata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ruguntsumi yayin da NLC ta garkame mambobin Majalisar Tarayya a Abuja, ta yi abu daya

Zanga-Zanga Ta Ɓarke a Kotun Ƙoli

A wani rahoton na daban Zanga-zanga ta ɓarke a Kotun kolin Najeriya kan hukuncin Kotun ɗaukaka kara na tsige ƴan majalisar tarayya na PDP da suka fito daga Filato.

Sun miƙa takardar adawa da matakin Kotun ga Alkalin alkalan Najeriya (CJN), mai shari'a Olukayode Ariwoola.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262