Arewa
Gwamnonin Arewacin Najeriya 19 sun gana da mai ba Shugaba Tinubu shawara a bangaren tsaro, Nuhu Ribadu yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da addabar yankin.
Yayin da aka dakatar da Sanata Abdul Ningi a Majalisar Dattawa, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya nuna goyon bayansa ga sanatan a kowane yanayi..
Tsohon shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum, Cif Gabriel Aduku ya rasu a yau Litinin, tsohon ministan lafiya ya rasu ne a kasar Amurka bayan fama da jinya.
Tsohon sanata da ya wakilci mazabar Nasarawa ta Yamma na tsawon shekaru 12, Abubakar Danso Sodangi ya riga mu gidan gaskiya a daren jiya Lahadi a jihar Nasarawa.
Yayin da aka shiga azumin watan Ramadana, Gwamna Ahmad Aliyu na jihar Sokoto ya amince da biyan rabin albashin ma'aikata domin gudanar da azumin cikin walwala.
Hukumar tace fina-finai ta Kannywood ta umarci rufe dukkan gidajen gala a fadin jihar Kano yayin da aka sanar da ganin watan azumin Ramadana a yau Lahadi.
Sarkin Musulmi na Sokoto ya bayyana cewa, an ga watan Ramadana a wasu jihohin kasar nan, kamar yadda rahotanni suka shaida daga jihohi daban-daban.
Gwamnonin Najeriya sun hada kai, sun bayyana yadda suka tsara kawo mafita ga duk wasu matsaloli da ake fama da su a kasar nan na karancin abinci da tsada.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa yara tara daga cikin 102 da kungiyar Boko Haram ta sace sun kubuta daga hannun ‘yan ta’adda a jihar Borno.
Arewa
Samu kari