Sanarwar Sarkin Musulmi: An Ga Wata a Wasu Jihohin Najeriya, Za a Fara Azumi Ranar Litinin

Sanarwar Sarkin Musulmi: An Ga Wata a Wasu Jihohin Najeriya, Za a Fara Azumi Ranar Litinin

  • Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin jaririn watan Ramadana na hijira ta 1445 daidai da 2024
  • Za a fara azumin watan Ramadana a ranar Litinin 11 ga watan Maris, inda al'ummar Najeriya da ma duniya ke murna
  • Kasar Saudiyya ma ta sanar da fara azumin na Ramadana, wanda za a yi azumin kwanaki 30 akalla a cikinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Jihar Sokoto - Sarkin Musulmi ya sanar da cewa, a ranar Litinin 11 ga watan Maris ne za a fara azumtar Ramadana a Najeriya.

ya bayyana hakan ne a wani sakon kai tsaye da aka wallafa a shafin hukumar ganin wata ta kasa da misalin karfe 8:40 na dare a ranar Lahadi 10 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Ramadan 2024: Muslman Najeriya na zuba ido kan ganin jaririn watan Ramadana

Wannan na nufin, ranar Litinin ce za ta zama ranar 1 ga watan Ramadana na hijirar Annabi SAW 1445, kamar yadda ya shaida.

Kalli bidiyon a kasa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ku taimakawa 'yan uwanku, Sarkin Musulmi ga attajirai

A bangare guda, sarkin ya yi kira ga al'ummar Musulmi masu hannu da shuni da su dubi yanayin da ake ciki tare da yiwa talakawa alheri.

Ya fadi hakan ne tare da rokonsu da cewa, su yi kokarin tallafawa ta fuskar abinci da abin da ba a rasa ba a watan na Ramadana.

Ya kuma yi kira ga 'yan kasa da su sanya Najeriya a addu'oinsu a cikin watan, inda ya yi addu'ar dawwamar zaman lafiya da saukin rayuwa.

Najeriya dai na ci gaba da shiga yanayin halin kakani-kayi kan yadda kayayyaki ke kara tashi da kuma yadda ake fuskantar matsalar tsaro a wasu yankuna.

Kara karanta wannan

Ramadan 2024: Hukumomin Saudiyya sun sanar da ganin jaririn watan Ramadana

An ga watan azumi a Saudiyya

A wani labarin, hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da za a fara yin Azumin watan Ramadana daga ranar 11 ga watan Maris na 2024.

Wannan na zuwa ne bayan da aka ga jaririn watan na Ramadana da yammacin yau Lahadi, 10 ga watan Maris, daidai da 29 ga watan Sha'aban 1445.

Ana sa ran, al'ummar musulmi a duniya za su fara Azumin na Ramadana, watan da kowa ke maida hankali ibada da neman kusanci ga Allah.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel